Shugaba Buhari ya umarci a hukunta sojan da ya kashe Sheikh Goni Aisami

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da abin da ya kira “kisan babu gaira-babu-dalili da aka yi wa Sheikh Goni Aisami” wanda ake tuhumar wani sojan Nijeriya da kashe shi bayan da shaihin malamin ya ya rage masa hanya a motarsa, kamar yadda ‘yan sanda suka tabbatar.

Yayin da yake mayar da martani kan lamarin, cikin wata sanarwa da kakakinsa Malam Garba Shehu ya fitar, shugaban ya ce “wannan mummunan kisan da sojan Nijeriya ya yi wa wannan mutumin kirkin da ya taimake shi ba hali ne da aka san sojojin ƙasar nan da shi ba, kuma ya yi hannun riga da horon da aka ba sojoji na nuna ɗa’a da girmamawa da kare rayukan waɗanda ba su aikata wani laifi ba.”

Shugaba Buhari ya ƙara da cewa, “a matsayina na babban kwamandan sojojin Nijeriya, na fusata matuƙa kan wannan mummunan aikin da jami’in tsaro da aka horas domin ya kare rayuka ya aikata.”

Ya kuma yi kira ga hukumomin sojin ƙasar “da su hukunta waɗanda suka aikata wannan ƙazamin laifin ba tare da ɓata lokaci ba, sannan su yi waje da ire-iren waɗannan sojojin masu mummunan hali.”

A qarshe ya miƙa saƙon ta’aziyya ga gwamnatin Jihar Yobe da jama’ar jihar da kuma iyalan Sheikh Goni Aisami.