Masarautar Lafiya ta naɗa Dr. Justina Kotso sarautar Tauraruwar Ilimin Matan Nasarawa

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

A ƙarshen makon da ya gabata ne Masarautar Lafiya, babban birnin Jihar Nasarawa ta naɗa wa shugabar makarantar Kimiyya da Fasaha ta gwamnatin jihar wadda aka fi sani da Isa Mustapher Agwai Polytechnic dake Lafiya, Dokta Justina Kotso sarautar Tauraruwar Ilimin Matan Jihar Nasarawa. 

Da yake jawabi jim kaɗan bayan ya naɗa wa shugabar makarantar sarautar, Mai martaba Sarkin Lafiya wanda shi ne kuma shugaban majalisar sarakunan gargajiyan jihar, mai shari’a Sidi Bage mai ritaya ya bayyana cewa masarautar ta yanke shawarar naɗa wa Dokta Justina Kotso sarautar ne bayan ta yi la’akari da kuma bibiyar gagarumar gudumawa da take bai wa ɓangaren inganta ilimi a jihar musamman ilimin mata da nakasassu. Shi ya sa aka naɗa mata sarautar. 

Ya taya shugabar makarantar kimiyya da fasaha ta Isa Mustapher Agwai mallakar gwamnatin jihar, Dokta Misis Justina Kotso murnar naɗin sarautar nata, inda ya buƙace ta ta cigaba da waɗannan ayyukan ɗaukaka fannin ilimin musamman na mata da take yi a jihar da ƙasa baki ɗaya, inda ya kuma tabbatar mata cewa a nasu ɓangaren masarautar Lafiya da majalisar sarakunan gargajiyan jihar baki ɗaya za su cigaba da ba ta cikakken goyon baya don ƙara mata ƙwarin gwiwa. 

Daga nan sai basaraken ya yi amfani da damar inda ya ƙalubalanci sauran manyan matan jihar baki ɗaya su yi koyi da kyawawan manufofin Dr. Justina Kotso na inganta harkokin ilimi musamman na mata a jihar wanda a cewarsa ke da matuƙar muhimmanci. 

A nata ɓangaren da take mai da martanin jawabi wacce aka naɗa wa sarautar, Dr.  Kotso bayan ta gode wa masarautar ta Lafiya ƙarƙashin jagorancin mai Martaba Sarkin Lafiya, mai Shari’a Sidi Bage dangane da zaɓin ta da suka yi a matsayin wacce ta fi dacewa da sarautar ta kuma yi alƙawarin ba za ta bai wa masarautar kunya ba. 

A cewarsa wannan sarauta ta Tauraruwar Ilimin Matan jihar Nasarawa baki ɗaya da aka ba ta zai kasance wani babban ƙalubale ne a rayuwar ta.

Kuma za ta cigaba da yin iya ƙoƙarin ta wajen tunkarar ƙalubalen musamman ta hanyar cigaba da ƙirƙiro tare da aiwatar da ingantattun shirye-shiryen ilimi da za su cigaba da kawo canje-canje masu ma’ana a rayuwar al’ummar jihar baki ɗaya musamman ‘yan uwanta mata, inda ta buƙaci masarautar da al’ummar jihar baki ɗaya su cigaba da bata cikakken goyon baya don cimma burin. 

Abubuwan da aka gudanar a wajen taron naɗin sun haɗa da naɗin sarautar da mai martaba sarki da kansa ya yi da fatan alheri daga abokai da ‘yan uwan Dr. Kotso. Yayin da su kuma a nasu ɓangaren makaɗa da maroka da mawaƙa suka nishaɗantar da taron.