‘Yan sanda sun yi ram da Alhassan Doduwa

Daga IBRAHIM HAMISU, Kano

‘Yan sanda sun kama Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, bisa zarginsa da hannu wajen kashe wasu mutane tare da ƙona sakatariyar jam’iyyar NNPP a yayin zaɓen da aka gudanar ranar Asabar.

Rundunar ‘yan sandan ta tabbatar da cewa aƙalla mutum uku ne suka mutu a lokacin da aka ƙona sakatariyar yaƙin neman zaɓen jam’iyyar NNPP da ke Tudunwada a Kano.

Mutane biyu ne suka ƙone ƙurmus a rikicin da ya ɓarke yayin tattara sakamakon zaɓen Majalisar Wakilai ta Doguwa/Tudunwada wanda a ƙarshe aka bayyana Doguwa ne ya lashe zaɓen.

Wata majiya mai tushe daga rundunar ‘yan sandan ta shaida wa Dailytrust cewa an cafke Doguwa ne a filin jirgin saman Malam Aminu Kano a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Abuja.

Majiyar ta ce rahoton da hukumar ‘yan sanda ta fitar a Tudunwada ya bayyana cewa Doguwa da kansa ya jagoranci ‘yan bangar siyasa suka ƙona sakatariyar NNPP inda aƙalla mutum biyu suka ƙone kurmus.

“Ya kuma yi amfani da bindigar dogarinsa tare da harbin kan mai uwa dawabi. Don haka mun kama shi da laifin kisa da ƙona waɗanda ba su ji ba basu gani ba,” in ji sanarwar

“A halin yanzu yana amssa tambayoyi a sashen binciken manyan laifuka na jihar Kano.”

Tun da farko, Doguwa a wata zantawa da manema labarai ya musanta zargin da ake masa, ya kuma ce ya samu labarin cewa ‘yan sanda na neman sa amma bai samu wata gayyata a hukumance ba.

Ya kuma musanta zargin cewa ya harbe wasu mutane da dama a rikicin da ya ɓarke, yana mai cewa shi ba shi da bindiga haka nan bai san harbin bindiga ba.

“Ban taɓa rike bindiga ba. Ban ma san yadda ake riƙe bindiga ba. Haka kuma ban taɓa riƙe wani makami ba a duk lokacin zaɓen,” inji Ado Doguwa.

Sai dai ya ce rikicin ya faro ne lokacin da magoya bayan jam’iyyar NNPP suka zo da nufin ƙona ofishin INEC kuma magoya bayan APC suka fatattake su.

An jiyo muryar ɗaya daga cikin waɗanda suka jikkata inda ya ce “Alhassan Ado da kansa ya harbe ni ba wani ya sa ba, kafa ya fasa min ƙafa”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *