Daga BASHIR ISAH
Hukumar kula da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta bai wa ‘yan wasan ƙungiyar hutun mako guda bayan da ƙungiyar ta samu nasarar zuwa Gasar Firimiyar Nijeriya.
Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da shugaban ƙungiyar, Babangida Umar, ya fitar jim kaɗan bayan kammala wasan ƙarshe na ƙungiyoyi takwas da ake kira da ‘super 8’ na Gasar Firimiyar Nijeriya wanda ya gudana a filin wasa na Stephen Keshi da ke Asaba, Jihar Delta.
Umar ya ce shugabannin ƙungiyar ba za su tafi hutu ba har sai sun miƙa rahotonsu na wannan kaka.
Shuganan kulob ɗin ya yi amfani da wannan dama wajen yaba wa gwamnatin jihar da ‘yan wasan da ma shugabannin ƙungiyar haɗi da magoya bayan ƙungiyar da sauran jama’a bisa goyon bayan da ake ba su wanda a cewarsa, hakan shi ne dalilin nasarar dawowa cikin Gasar Firimiyar Nijeriya da ƙungiyar ta samu.
Tare da shan alwashi kan cewa, za a yi dukkan mai yiwu domin tabbatar da nasarar ƙungiyar a gasar ta firimiya.