Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Me ma za a ce ne kan dimokraɗiyyar Nijeriya musamman daga dawowa mulkin farar hula a 1999 kan wani canji na masu damawa a sha ko a na so ko ba a so. Kusan canjin a can sama ba yawa sosai don bayan mulkin PDP a 2015 da ta samu shekaru 16 an samu sabon shugaba da bai yi PDP wato Muhammadu Buhari amma sauran muƙarrabansa za ka taras akwai da yawa waɗanda jihohin PDP ne su ka kauro zuwa APC.
In sharri PDP ta yi irin waɗannan mutanen na da kason su. Mu ma duba shi kan sa shugaba Buhari ai tsohon shugaban mulkin soja ne bayan kifar da gwamnatin dimokuraɗiyya ya zo ya dare karaga karo na biyu. Mu koma baya shi ma tsohon shugaba Obasanjo ai ya yi mulkin sojan na tsawon shekaru tun bayan kisan gilla ga Janar Murtala a 1976 zuwa miƙa ragama ga marigayi Shehu Shagari a 1979.
Cikin waɗanda su ka mulki Nijeriya zuwa yanzu in ba tsohon Janaral na soja za ka samu ɗan uwan wani Janaral ɗin ne ko aƙalla a ce wanda wani Janaral ya ɗaure wa baya. Shin shi sabon shugaba Bola Ahmed Tinubu wa ya xaure ma sa baya?
Bayanai da sharhin mu zai iya gano ma na yadda lamarin ya ke. Kafin na aara tsunduma bayanai mun tabbatar Tinubu ya samu mara baya daga manyan ‘yan jari hujja da in akwai mafi qaramin muƙami a cikin su su ne gwamnonin da ke kan gado.
Wataƙila wani ya yi tunanin me ya sa zan ambaci gwamnoni da ƙanana a ciki sai in ce wasu gwamnonin na da iyayen gidan da kan ɗaure mu su baya kuma sun fi su tasiri don ba mamaki sai da su ka yi mulki na tsawon shekaru 8 kafin shiga Majalisar Dattawa ko karvar manyan mukamai a tarayya ko kuma ya zama sun zama iyayen gidan siyasa don tarin dukiyar da su ke da ita.
Jagororin nan a yanzu ma maimakon su ƙarfafa wa sabbin fuskoki sai ya zama su na ƙoƙarin turo ‘ya’yan su da matan su majalisa ko muƙaman ministoci da sauran manyan ma’aikatun gwamnati. Ka ga dimokuraxiyya a Nijeriya na neman juyewa zuwa ta DIMULUKIYYA wato gamayyar dimokraɗiyya da mulkin gado na mulukiyya. In ka ga wani na daban ya ratso cikin tawagar waɗannan mutanen to ya zama zakkah kuma in bai dage ba sai ya bi shanun sarki ko ya zama ɗan a bi Yarima a sha kiɗa.
Kasancewar talauci da ya ƙanƙame talakawa ba sa iya jajircewa ko akasarin su ba za su iya jajircewa su ɗora nagartattu ko zaɓin su a kan muƙaman siyasa ba. Ai an samu bayanan yadda kuɗi ya sauya ra’ayin mutane a wasu jihohi a lokacin babban zaɓen da ya gabata.
Za ka ga mutane na ta ƙorafi da hankoron samar da canji amma da zarar waɗanda su ke son canjawa sun turo ‘yan sulallan cefane sai lamari ya canja ka ji a na cewa “kowa ya bi; ko ba ka bi ba an bi ma ka” Al’adar ‘yan siyasa ne idan sun kashe maƙudan kuɗi wajen sayen goyon bayan jama’a to za su juyawa jama’ar baya lokacin da su ka dare kujera kuma ba lalle a ce sai sun yi sata ba ma’ana aqalla za su guji jsma’ar har sai in lokacin sake neman ƙuri’a ya zagayo sai su sake dawowa su sake miƙa wa mutane na cefanen kwana biyu.
Kai talauci musiba ce amma mafi girman musiba talaucin zuciya!
Biyo bayan sauke akasarin manyan jami’an tsohuwar gwamnatin Buhari, yanzu hankali ya koma kan naɗa majalisar zartarwa ta sabuwar gwamnatin Bola Tinubu. In za a tuna an kwashe lokaci mai tsawon gaske a 2015 kafin tsohon shugaba Buhari ya naɗa ministoci kuma wasu tun da a ka naɗa su ba su bar gwamnati har sai da Buhari ya kammala wa’adin mulkinsa a ranar 29 ga Mayun da ta gabata.
Akwai ’yan misalai ƙalilan ainun na ministocin da ba su yi nisan zango ba da in na ce Sano Nanono da Saleh Mamman na cikin su. Mafi ƙaranci a sauran su ne waɗanda su ka yi wa’adin farko ba su dawo na biyu ba kamar Janar Abdulrahman Dambazau, Augu Obbeh da Solomon Dalung. Wasu kuma dalilan samun wani muƙamin ya sa su ka bar gwamnatin kamar Amina Muhammad da ta tafi Majalisar Ɗinkin Duniya da Usman Jibrin da ya zama Sarkin Nasarawa.
Don haka a gaskiyar magana ministocin gwamnatin Buhari na daga mafi samun damar ministoci tun ba wa Nijeriya ’yanci wajen sakin mara don su yi aikin da ya kamata kuma in ma ba su yi yadda ya kamata gazawar daga gare su ne ko daga shugaban da ya zuba mu sui do ne.
Rahotanni na nuna masu neman muƙaman minista da manyan masu ba da shawara daga tsohuwar gwamnatin na da yawan gaske kuma a halin yanzu na kamun kafa don samun gurbi a sabuwar gwamnatin.
Muqarrabin shugaba Tinubu wanda ya yi riƙon takarar mataimakin ɗan takara kafin ayyana sunan Kashim Shettima wato Ibrahim Kabir Masari ya ce, ya na da kwarin gwiwar za a yi sabon zubi a wajen muƙaman.
Masari ya ce, duk da wasu da dama a tsohuwar gwamnatin Buhari na bin kafa don sake dawowa kan kujera; hakan na da wuya ainun.
“Duk wanda ya riqe muƙami atsohuwar gwamnatin Buhari ya dace ya koma gefe ya rungumi wata sana’ar don ba wa wasu damar gwada ta su basirar” Inji Masari da ya ba da labarin tun bayan ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zave ministocin su ke da zuwa majalisar Tinubu don neman a yi tafiya da su. Masari ya ce da ya ke su kan zauna hirar dare a wajen Tinubu su kan ga masu kamun kafar na shigowa don su nuna su na tare da Tinubu.
A shawarar Ibrahim Masari kamar yadda tsohon shugaba Buhari ya koma gefe bayan sauka daga mulki duk waɗanda su ka yi aiki da shi su ma su bi sahun sa wajen komawa gefe ko shiga wata sabgar su bar fagen ga wasu sabbin fuska don su kawo wani tsarin na daban.
Mukarrabin na Tinubu ya nuna mamakin ga waɗanda ke nacin sai an cigaba da damawa da su a gwamnati cewa bai ga mene ne su ka manta a fadar Aso Rock da su ke son ɗaukowa ko sake bita ba bayan damar shekaru takwas su na toya wainar su.
Lauya mai zaman kan sa a Abuja Auwal Abdulkadir Albarudi ya shawarci shugaba Tinubu ya raba gwamnatin sa da jami’an gwamnatin Buhari don hakan ne zai ba shi damar naɗa na sa mutanen don samun sauyi daga waɗanda a ke zargi da almundahana.
Albarudi ya ce, ai yadda jami’an gwamnatin Buhari su ka yi aiki ba a ce mu su kanzil to haka za su ɗauka in an ba su dama a sabuwar gwamnati don haka ba wani sabon abu da za a iya cimmawa.
Lauyan ya ƙara ba wa tsoffin ministocin shawarar komawa gefe su bar wasu da ba mamaki ma sun fi su ilimi da kwarewa don kawo na su salon da zai iya kawo canji da zai amfani miliyoyin ’yan Nijeriya. Har ma ta kai ga lauyan ya kawo wata aya a Alkur’ani da ke magana kan wasu mutane da za a zo lahira a ce mu su sun cinye rabon su a duniya don yanda su ka samu damar shuka alheri amma su ka aikata akasin hakan.
In za a tuna dai tsohon shugaba Buhari bai yi alwashin tsayawa mutanen sa ba da kai tsaye ya ke nufin kowa ya debo da zafi bakin sa. Kamar tsohon shugaban ya hango za a iya zuwa yanayin irin abun da mu ke gani yau inda jami’an DSS su ka cafke dakataccen gwamnan babban banki Godwin Emefiele da riƙe shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa Abdulrasheed Bawa.
“Duk wanda ya neme ni na ba da wata shaida a kan sa a kotu to kowaye ne ya yi kuka da kan sa” Inji tsohon shugaba Buhari. Masu yi wa tsohon shugaba Buhari adalci na cewa sai dai a kama shi da salon kyaliya ko rashin bin sawun jami’an sa amma a karan kan sa bai ci amanar baitul malin Nijeriya ba.
Kazalika wasu na ɗora laifin rashin matakai masu tsauri na Buhari da jinya da ta same shi a wa’adin mulkin san a farko.
Tsohon shugaban dai na London da wasu mafi kusaci a mukarraban sa waɗanda in ka gan su a waje to ba mamaki tsohon shugaban na kusa.
Kammalawa;
Yanzu dai lokaci zai nuna yadda gwamnatin Tinubu za ta kasance duk da an ga yadda ta karya da cafke madugun babban banki da ya faro daga gwamnatin tsohon shugaba Jonathan.
Kuma duk wanda Allah ya ba wa wani muƙami to ya yi ƙoƙari ya shuka alheri iya iyawar sa kar a same shi da cin amana da kasala don kuwa mulki irin na dimokraɗiyya ya na da wa’adi kai ba ma wa’adin kare mulkin ko sake yunƙurin samun sabon muƙami ba, da kirki da rashin kirki akwai wa’adin qarshe na zama a shi kan sa doron ƙasa.