Daga BASHIR ISAH
An karrama ma’aikaciyar Jaridar Blueprint, Ene Oshaba da lambar yabo ta ‘ReportHer Award’ bayan da ta yi zarra a tsakanin takwarorinta mata ‘yan jarida su sama da 100.
An karrama Ene ne a matsayin ‘yar jaridar da ta yi rubuce-rubucen da mata suka fi amfana da su
Tashar Radio 91.7 tare da haɗin gwiwar United Women for ECOWS da cibiyar aikin jarida na bincike ta Wole Soyinka (WSCI) tare da Gwamnatin Kanada ne suka ɗauki nauyin shirin.
Shugabar tashar Women Radio, 91.7, Toun Okewale Sonaiya, ta ce an ƙirƙiro shirin ne don amfanin mata da kuma rajin shigar da mata cikin harkokin gina ƙasa.
Ta ce, “Shirinmu na rediyo da sauran ayyukan tallafi sun maida hankali ne a kan mata ɗari bisa ɗari inda mata kashi 90 sun amfana.
“A 2015 muka assasa taron Voice of Women Confereance (VOW), taron da kan tattaro ƙungiyoyin mata daban-daban wuri guda kan manufa ɗaya don cigaban ƙasa.
Shugabar cibiyar WSCI, Motunrayo Alaka, ta bayyana cewa cibiyar ta tallata aikin jarida na bincike a Nijeriya domin ƙarfafa dokoki da tabbatar da adalci da walwalar jama’a.
“WSCI ta horar da ‘yan jarida sama da 4,000 daga kafofin yaɗa labarai sama da 180 a sassan daban-daban,” in ji ta.