Shin motsa jiki na taimako ga matsalar damuwa?

Daga AISHA ASAS

Masu karatu barkanmu da sake saduwa a shafin kwalliya na jaridar al’umma, Manhaja, da fatan ba ku ƙosa da wannan darasi na atisaye ba.

A yau da yardar mai dukka za mu taɓo wani ɓangare da kusan zan iya cewa ya fi adabbar mutane, amma rashin sani kan sa ayi masa wata fassarar da ta saɓa wa sananniyar ma’anar sa.

Da yawa daga cikin wasu matsaloli da suka dangance ciwo da muke cewa matsala ce ta mutanen ɓoye, ko sammu da jifa, zuwa duk wata damuwa da ta shafi rikeɗewar tunani, takan samu ne ta sanadiyyar damuwa.

Ita damuwa ciwo ce mai zaman kanta da take haifar da alamomi da suke kamanceceniya da tavin hankali ko bugun aljanu. Rashin amincewa da akwai cuta da ake samu sanadiyyar damuwa ya sa muke wahala sosai da ita, kuma ta ke mana illa fiye da sauran waɗanda suka yi imani da ita.

A Ƙasar Hausa da yawa sun ƙi amincewa da cutar bare har su amince da nema mata magani, kuma bincike ya tabbatar da cewa, a cikinsu ne aka fi yawaitar samun waɗanda ke kamuwa da cutar, sakamakon hanyoyi da dama na kawar da dumuwa sun barranta da su, kuma suna a layin farko wurin musanyyar matsalolin da ke haifar da damuwa a tsakaninsu.

Idan mun ɗauki matsalar zamantakewar aure, kamar yadda masana suka tabbatar bayyana damuwa ga wani na ɗaya daga cikin magungunan da ke hana ciwon damuwa tasiri, wannan ne ya sa Bature ya yi tanadi na musamman kan ilimin sauraron mutane don jin damuwarsu da kuma ba su shawarwarin inda ya kamata su dosa, wato therapy a turance.

Abin tambaya anan, mutum nawa ne a cikinmu suka amince da wannan a matsayin mafita? Kuma mutum nawa ne suke ba wa makusantansu damar bayyana damuwarsu a duk lokacin da aka yi masu abinda ya sosai zuciyarsu?

Matsalar damuwa dai matsala ce da ke tava ɓangaren ƙwaƙwalwa, don haka za mu iya kiranta da matsalar ƙwaƙwalwa a kai-tsaye, yawaitarta kuwa zata iya kai ga samuwar alamomi na mai tavin hankali.

Kasancewar darasinmu na yau ba kan bayanin matsalar ta damuwa ba ce, don haka ba za mu zurfafa kanta ba, za mu je kai tsaye ga amsa tambayar darasin namu, wato tasirin atisaye ga mai fama da matsalar damuwa.

Bincike mai inganci da aka yi, daga Cochrane, wanda ya yi amfani da sakamakon gwaje-gwajen da ƙasashen duniya ta yi kan wannan lamari, ya ayyana cewa, motsa jiki na da gudunmuwar da yake bayarwa wurin kawar da damuwa, sai dai ba taimako ne mai yawa sosai ba da yakai adadin wanda yake bayarwa a wasu gaɓoɓin jiki ba.

Sai dai ƙarancin sa ba zai sa a kira shi da marar amfani ba, domin da kaɗan ɗin idan an haɗa a wata hanya daga cikin hanyoyin kawar da damuwa za a iya samun kyakkywan sakamako.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *