Dandalin shawara: Mijina ba ya son haihuwa

Daga AISHA ASAS

TAMBAYA:

Salam. Ina wuni Asas. Allah Ya taimake ki ga dukan lamuranki. Ki taimake ni, yadda Allah ya taimake ki. Mijina da muka yi aure da shi shekara takwas.

Da aka kawo ni gidanshi, kullum sai ya ba ni magani zai kusance ni, bai taɓa fashi ba, sai da na yi shekara biyu da aure, har shan maganin ya ishe ni, amma ko na yi ƙorafi sai ya rarrashe ni, idan na ƙiya sai ya ƙi kusanta ta ko da kuwa ya matsu da son yi.

To da iyaye suka fara zancen ba mu haihu ba, mu tafi asibiti, shi ne fa ya sanar da ni ba ya son haihuwa, kuma maganin da yake ba ni na kar na ɗauki ciki ne.

Da daɗin baki ya yaudare ni na biye ma shi har muka ƙara shekara biyu. Da hankali ya saukar min sosai na fara tunanin abinda zai faru gaba idan na ci gaba da rayuwa a haka.

Ana nan sai likitan da muke zuwa ya bada shawarar na yi tsarin iyali da ake yi a asibiti, don maganin bai kamata na ci gaba da shan shi ba. Ko na sa roba, ko a ɗaure bakin mahaifa da dai wasu da ya yi bayani. Shi ne fa da na dawo na shaida ma wata abokiyata, ta gaya min akwai yiwar na samu matsala idan na yi a gaba.

Ba ma shi ya fi tada min da hankali ba kamar da ta ce akwai yiwar na samu kansa idan na yi, to kuma muna da kansa a gidanmu kinga ina samun ta cikin sauƙi. To da na gaya mishi mu nemi wata mafita ba wannan ba, shi ne fa ya ce babu wata hanya idan ba wannan ba, kuma dole zan zaɓa, ko yin ko kuma a bakin aurena.

Kuma ya gaya min Allah zai yi fushi da ni idan har na yi sanadiyyar mutuwar aurena da kaina, kuma zai iya ma zama silar shiga ta wuta, don Annabi Muhammad Sallallahu allaihi wa salam ya ce, macen da ta nemi saki daga mijinta ko ƙanshin aljanna ba za ta ji ba.

Wallahi ban san abin yi ba, shi ne na ce bari na neme ki, don na ga shawarar da ki ka ba wa wata a facebook sati uku da suka wuce. Allah Ya biya ki da aljanna.

AMSA:

Amin, Ina godiya. Da farkon fari dai zan fara da haihuwar ita kanta, duk da cewa neman shawarar taki ba ta karkata ɓangarenta ba sosai. Shin me ya sa ake yin aure?

Don a samu natsuwa ta hanyar kawar da sha’awa ta sahihiyyar hanya, da kuma samun zuri’a, wato haihuwa. Idan kuwa haka ne, kinga ke riba ɗaya ki ka samu cikin biyu, wato dai ba ki da ribar samun ƙaruwa.

Gava ta biyu, a matsayinki ta mace, kin tava zama ki ka yi dogon tunani kan inda ki ka dosa? Ko tambayar kanki makomarki yayin da ki ka sake wankin hula ya kai ki dare, wato ki ka wuce shekarun da aka fi sa ran samun haihuwa?

Yaushe ne ƙarshen rashin buƙatar haihuwar da mijinki ke yi? Shin a na ki ra’ayin za ki so ki yi rayuwar har ƙarshe ba tare da kin mallaki ɗa da za ki iya kira da naki ba? yayin da ki ka ci gaba da biyewa mijinki, kina ƙayyade iyali na ba ƙyaƙyautawa ya makomar lafiyarki da damar da ki ke da ita ta samun haihuwa?

Idan har ba ki wa kanki waɗannan tambayoyin ba, kuma ki ka ba wa kanki gamsassun amsoshi da zuciyarki ta tsayu kansu, zan iya cewa, ba ki san inda alƙiblar rayuwarki ta dosa ba, kuma ba ki yi wa rayuwarki tanadin jin daɗin zaman duniya ba.

Ba zan iya illata tsarin iyali a kai-tsaye ba, domin kowa da irin dalilin da yake sa shi ya yi, kuma bayyanai daga wasu malamai sun sasauta lamarin har suke kawo wasu dalilai da suka halasta shi, sai dai irin naki kai tsaye zan buga mishi guduma, zan kira shi da son zuciya wanda ke tare da ɓacin ta, musamman ma kasancewar ke kina bin ra’ayin mijinki ne kawai babu tabacin hakan zai iya zama zaɓinki idan ki ka samu dama.

Addinin Musulunci ya hana ƙyamatar haihuwa, kamar yadda hadisi ingantacce daga wurin fiyayyen halitta, annabin rahma cewa, “ku yi aure, ku haifafa, domin in yi alfahari da ku ranar tashin ƙiyama.” Kinga kuwa kusan haihuwa ce jagaban tafiyar.

Abu mafi muhimmanci shi ne, sanin matsayarki kan hukuncin da mijinki ya yanke maku, shin ke ma ba ki buqatar haihuwar ce, wanda hakan zai sa ki girbi abinda ki ka shuka ba wanda aka shuka ma ki ba.

Abu na gaba, amfani da ababen da ke hana samun ciki a matsayinki ta mace, idan na fara da maganar zancen da ki ka yi na ciwon daji da ku ke da shi a zuri’arku, tabbas masana da dama sun tabbatar da allura ko saka robar tsarin iyali na ƙara yiwar kamuwar cutar kansa ga wanda yake da ita ta gado, kuma tana iya zama silar kamuwa da cutar koda babu ita a zuri’ar.

Za mu ci gaba mako mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *