A nisanta yara daga hotuna da bidiyon batsa

Na san wannan take na yau zai tayar da hankalin wasun mu da dama, musamman malamai, alarammomi da ɗaliban ilimi, da ma uwa uba iyaye. Ba na zavi in yi wannan faɗakarwa kan almajirai ne kaɗai ba, har ma da sauran yaran mu da ke rayuwa a gaban iyayensu.

Na san ba ni kaɗai ne wannan al’amari ke damuna ba, lura da yadda ake cigaba da samun taɓarɓarewar tarbiyyar yara ƙanana da ke samun kansu a cikin wata irin gurvatacciyar rayuwa marar tsafta, saboda rashin kulawar iyaye, sa ido daga manya masu kula da tarbiyya, har ma da malamai da ake bai wa amanar kula da ba su kyakkyawar tarbiyya da ilimantarwa.

Babu shakka akwai abin tashin hankali da damuwa ka ga yaro ƙarami wanda ake sa mai rai da zama malami, kuma jagora nan gaba idan Allah ya ja kwana, a ga ya taso yana wasu halaye da ba su kamata ba, ko kuma yana shiga inda ke da haɗari ga tarbiyyarsa da rayuwarsa.

Kuma na san babu wani malami ko uba da zai ji daɗin ganin ɗan sa ko ɗalibin sa yana aikata wani abu da al’umma za ta yi tir da shi. Sai dai wani lokaci babu yadda mutum zai iya, don kuwa ko da kana yin naka ƙoƙarin a gida ko a makaranta, abokai, ko al’umma da muhallin da yaro ke rayuwa a ciki, suna da gudunmawar da suke bayarwa wajen warware abin da ka ke ƙullawa na alheri a rayuwarsa.

Wani abin takaici da ya ke faruwa a yanzu shi ne na yadda wayoyin hannu masu ƙirar android suka yi yawa a hannun yara, saɓanin a shekarun baya. Yayin da wasu iyayen ke saya wa yaransu da kansu don su riƙa tuntuvarsu a duk inda suke, wasu kuma suna saya musu ne don ya taimaka musu wajen aikin makaranta, ko kuma don gata, da burgewa.

Sai dai a yayin da aka bai wa yara masu qananan shekaru waya ko waɗanda suke cikin shekarun balaga, mai ake tunanin za su iya yi da waɗannan manyan wayoyi?

Wani bincike da aka gudanar ya bayyana cewa, yaya qanana da suka damar kallon bidiyon batsa da wasu finafinai da ba su kamata ba, suna iya tasowa da wasu halaye da za su iya cutar da rayuwarsu da alaƙarsu da sauran jama’a, musamman alaƙar mace da namiji. Yara maza za su iya tashi da jarabar son mata, ko halayyar kin daraja ’ya mace da wulaqanta ta ko cin zarafinta da yi mata fyaɗe.

Haka ma a vangaren mace za ta iya tashi da rashin sakewa da mutane, tsoron namiji ko kai kanta ga inda za a wulaƙanta rayuwarta da mutuncin ta na ’ya mace, don tana ganin hakan shi ne soyayya.

Ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, wasu iyaye masu tsauri da sa ido da yayye masu wayewa kan harkokin rayuwa sun sha bayyana yadda suke ganin wayoyin yaransu ko ƙannensu cike da bidiyo da hotuna marasa kyan gani, da ke nuna tsiraici da yadda mace da namiji ke saduwa tsirara, da sauran abubuwa na batsa. Wa’iyazubillah!!!

Wani ya taɓa ba da labarin yadda wata ƙanwarsa ke shiga manhajar Google ko YouTube a babbar wayar da aka saya mata don aikin makaranta a ɓoye, don kallon bidiyon batsa, da tunanin ba za a gane ba, amma saboda yana da ilimin gano waɗannan sirruka, ba tare da ɓata lokaci ba ya gano abin da take yi, har kuma ya ja hankalin iyayensu kan abin da ke faruwa.

Wasu yaran a makarantar ne ma suke haɗuwa da abokai ko ƙawayen da suke tura musu irin waɗannan munanan hotunan batsa da bidiyo suna ɓoyewa a waya suna kallo.

Waɗannan ga yaran da ke gaban iyayensu a gida kenan kuma suke samun gatan karatu, to yaya kuma ga wasu yaran da ba su kai waɗannan shekarun ba ko kuma ba su ma samu gatan shiga makarantar boko ba, kamar almajiran da na yi magana a baya? Ko ba ka tava ganin yaran almajiran da aka kama wayoyinsu da irin waɗannan hotuna da bidiyon batsa ba?

A yayin nake haɗa wannan rubutu a wata anguwa cikin birnin Kano, wasu mutane sun lura da gungun wasu yara almajirai sun zagaye wani yaro a tsakiyarsu suna kallon wani abu a waya suna dariya, dubawar da suka yi kuwa sai ga shi suna kallon wani bidiyo ne na batsa, da ke nuna wasu mace da namiji suna lalata da juna.

Iyaye su ji tsoron Allah, su kula da makomar rayuwar ’ya’yansu, in har bai zama dole ba, su daina barin manyan wayoyin da za a iya tura hotuna ko bidiyo a hannun yaransu, in dai ba wanda za a amsa kira ba, in ma saboda yin aikin makaranta ne, a bari idan sun dawo gida sai su yi amfani da wayar maman su ko babansu ko wani yayansu da ke gida. A daina bari suna fakewa da saka manhajojin wasanni na ɗebe kewa ne ko sa karatun Alƙur’ani a ciki.

Sannan in ta kama tilas a bar su da babbar waya, akwai wasu hanyoyi da iyaye za su kulle duk wani shafi mai tura bidiyo ko hotunan batsa ta yanar gizo daga wayoyin yaransu, don kada shiga wayoyinsu nemo irin waɗannan shafukan batsa suna kallo.

Lallai ne malaman makarantun boko da na allo su qara tsaurara matakan hana yara zuwa makaranta da manyan wayoyi da ƙwace duk wata waya da aka gano ana yin abin da bai kamata ba.

Shugaban Ƙungiyar Malaman Tsangaya, Gwani Jibrin Yahaya ya yi kira ga malaman makarantun allo su ba da haɗin kai a ƙoƙarin da ƙungiyar ke yi na tsaftace harkar karatun allo, da shigo da tsare-tsaren zamani da za su kawar da ƙyama da tsangwamar da ya ce ana nunawa almajirai da makarantun tsangaya.

Daga MUSTAPHA MUSA, 08168716583.