Yanzu-yanzu: INEC ta ce za a yi ‘inconclusive’ a Kano

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana zaɓen ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Takai a majalisar dokokin jihar Kano a matsayin ‘inconclusive’.

Jami’in hukumar, Farfesa Usman Ibrahim na Jami’ar Bayero, Kano, ne ya bayyana hakan a ofishin INEC da ke Takai a ranar Lahadi, 19 ga Maris, 2023.

“Duk da cewa ɗan takarar jam’iyyar APC, Musa Ali ya samu ƙuri’u 24,573 yayin da ɗan takarar jam’iyyar New NNPP ya samu ƙuri’u 23,569, amma har yanzu ba mu da wani zaɓi da ya wuce mu bayyana zaɓen a matsayin ‘inconclusive’.

“Wannan ya faru ne saboda an soke zaɓukan da aka gudanar a rumfunan zaɓe biyar saboda yawan kƙri’u.

“Yanzu, za a sake gudanar da zaɓen a rumfunan zaɓe biyar da abin ya shafa,” in ji Ibrahim.

A wani labarin kuma, INEC ta bayyana Garba Gwarmai na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen mazabar Tsanyawa/Kuchi a majalisar dokokin jihar Kano.

Farfesa Ganiyu Shokobi, jami’in zaɓe na mazaɓar Tsanyawa/Kunchi ne ya sanar da sakamakon zaɓen a cibiyar tattara bayanai na hukumar da ke Tsanyawa.

Shokobi ya ce, Gwarmai ya samu ƙuri’u 31,471 inda ya doke abokin hamayyarsa Mohammed Ali na jam’iyyar NNPP, wanda ya samu ƙuri’u 27,864, yayin da Bello Abdullahi na PDP ya samu ƙuri’u 136.

Haka kuma a ranar Lahadin da ta gabata ne INEC ta bayyana sakamakon zaɓen mazaɓar Shanono/Bagwai.

Farfesa Ahmed Iliyasu ya bayyana Ibrahim Kundila na APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan ya samu ƙuri’u 38,021, yayin da Musa Aliyu na NNPP ya samu ƙuri’u 29,983.