Yari da Marafa ’yan bindigar siyasa ne a Zamfara, cewar Sani Shinkafi

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Ɗan takarar shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Alhaji Sani Abdullahi Shinkafi ya caccaki tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari da Sanata Kabiru Garba Marafa kan gudummawar da suka bayar na taɓarɓarewar jam’iyyar APC a jihar Zamfara, yana mai bayyana su a matsayin ‘yan bangar siyasa.

Shinkafi ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai a Gusau ranar Lahadi, a lokacin da yake mayar da martani ga ɓangaren Yari da Sanata Kabiru Marafa kan taron mazaɓun jam’iyyar APC da aka kammala a mazavu 147 na jihar.

A cewar sa, ƙaurace wa taron da ɓangaren Yari da kuma ikirarin yin zaɓe da ɓangaren Sanata Kabiru Marafa ya ce ya yi, ya yi wata maƙarkashiya ce na kawo cikas ga gwamnatin jihar a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Bello Mohammed Matawalle, na ƙoƙarin gina jam’iyyar zuwa babban matsayi a shekarar 2023.

“Ina so in bayyana ƙarara cewa, matakin da  angaren tsohon Gwamna Abdulaziz Yari da Sanata Kabiru Marafa suka ɗauka shine ake kira da ’yan bindigar siyasa a jihar Zamfara, kuma dole ne shugabannin hedkwatar jam’iyyar APC ta ƙasa su ɗauki mataki a kansu,” Shinkafi ya bayyana.

Ya bayyana cewa an gudanar da taron gundumomi da aka kammala cikin lumana kamar yadda hedkwatar jam’iyyar APC ta ƙasa a jihar ta ba da umurni.

Ya kuma bayyana ɓangaren Yari da ɓangaren Sanata Kabiru Marafa a matsayin waɗanda ba su dace da tsarin dimokraɗiyya ba.

“Ɓangaren Yari da Sanata Kabiru Marafa haramtattu ne kuma sun saɓa wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC, kuma shugabannin jam’iyyar APC na qasa ya kamata su ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki a kansu domin kawai suna ƙoƙarin kawo cikas ga jam’iyyar ne a Zamfara,” ya ce.

A cewarsa, shugabancin hedikwatar jam’iyyar APC ta ƙasa ta amince da taron gundumomin da aka gudanar a jihar Zamfara a ranar Asabar ɗin da ta gabata, inda ya ce babu wani zagon ƙasa ko maƙarƙashiya da ɓangaren Yari da Sanata Kabiru Marafa za su iya yi da zai iya rushe halastattun shuwagabannin.

“Babu wani zagon ƙasa da  angaren Yari da Marafa ke iya yi da zai iya shafar shugabancin jam’iyyar APC na maza un jihar Zamfara 147, kuma a shirye muke mu fuskance su a gaban kotu,” Shinkafi ya bayyana.