An nemi manoma su daina sarrafa amfanin da ke sanya cuta

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

An buƙaci manoma da su kiyaye da yadda za a sarrafa kayan amfanin gona bayan sun yi girbi domin kawo ƙarshen yadda a wani lokaci abincin ya kan zama sanadiyyar jawo cututtaka ga al’umma, matuƙar ba su yi amfani da shawarwarin masana harkar noma ba.

Farfesa Sani Miko, Shugaban Hukumar Sasakawa ta Nijeriya ne ya yi wannan kiran a yayin da ma’aikatar sa ta Sasakawa ta shirya wata bita mai taken ‘hada-hada kan kayan noma bayan girbi da kuma yadda za a ajiye shi.’

Ma’aikatar ta shirya bitar ne ga manoman jihar Kano da take aiki da su a faɗin jihar, a cikin shirin ta na bunƙasa noma da kiwo wanda ake yi wa laƙabi da (KSDP), shirin da gwamnatin jihar Kano tare da tallafin Bankin Bunƙasa Addinin Musulunci da ke Jidda (ISDB) da kuma Cibiyar Tallafar Rayuwa (LLF). 

Farfesa  Miko ya ce yanzu lokaci ya yi da manoma za su kiyaye abinda suka saba aiwatarwa na ɓarnatar da amfanin gona. Ya ce za su iya haxa kansu a ƙungiyance su girbe amfanin gonar su ta hanyar yin amfani da injin zamani.  

Miko ya ce dole ne manoma su kula wajen ajiye abinci domin kiyaye irin su ruma da makamantan su, domin yin hakan na iya haifar da cututtuka daban-daban ga ‘yan adam. Don haka ya shawarce su da su dinga tuntuɓar malaman gona don karɓar shawarwarin da suka dace. 

A nasa ɓangaren Kwamared Abdulrashid Hamisu Ƙofar Mata, wanda shine shugaban aikin KSADP a hukumar Sasakawa, ya ce tun farkon daminar da ta gabata sun yi wa manoma bita akan yadda za su yi noma na zamani, don haka a daidai wannan lokaci ya zama wajibi, tunda kwalliya ta biya kuɗin sabulu, a yi bitar ga manoman yadda za su adana amfanin gonar a zamanance, ta hanyar da ba zai lalace ba kuma ba zai yi illa ga jama’a ba.

Ƙofar Mata ya buqace su da su tabbatar in sun koma ƙauyukan su, su tabbatar sun ilimintar da ragowar ‘yan uwan su manoma. 

Bitar an gudanar da ita ne a wurare guda uku da suka haɗa da Ɗakin karatu na Murtala Muhammad, Ma’aikata Horar da Aikin Gona da ke Kadawa da Tukwi.

Mahalarta taron sun bayyana jin daɗin su tare da alƙawarin yin amfani da abinda suka koya a wajen bitar, haka zalika sun bada tabbacin yaɗa ilimin ga sauran al’umma na lungu da saƙon faɗin jihar Kano.