Yawan tashar sadarwa ta 5G da Sin ta gina ya kai kusan miliyan 2

Daga CMG HAUSA

Jami’in hukumar kula da aikin sadarwar ta ma’aikatar kula da masana’antu da aikin sadarwa ta ƙasar Sin Wang Peng ya bayyana a gun taron manema labarai da aka yi yau Talata cewa, yawan tashoshin sadarwar 5G da Sin ta gina, sun kai miliyan 1 da dubu 854, daga cikinsu ƙarin sabbin tasoshin da aka gina a watannin Afrilu da Mayu da Yuni ya kai kusan dubu 300, matakin da ya tabbatar da cewa, duk wata gunduma na iya kama da sakwani na 5G, yayin da kowane ƙauye ke iya kama layin Intanet.

Raya manyan ababen sadarwa, ya dasa harsashe wajen bunƙasa tattalin arziki na zamani. A watanni 6 na farko a bana, an samu saurin bunƙasar yin sayayya a intanet da ba da ilmi da jiyya ta intanet, kana an raya sha’anin yanar gizo ba tare da wata tangarda ba.

Ya zuwa ƙarshen watan Yunin bana, jimillar kuɗaɗen shigar da aka samu a fannonin ƙera kayan laturoni na zamani da samar da manhajoji da aikin sadarwa da kuma Intanet ta wuce kuɗin Sin Yuan triliyan 10.

Fassarawar Amina Xu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *