Yukren, ba ma fatan yaƙin duniya na uku

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

An yi yaƙin duniya na ɗaya da na biyu inda a ka yi asarar rayuka da dukiya don haka sam ba a fatan yaƙin duniya na uku. Yaƙin duniya na ɗaya daga 1914-1918 ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji miliyan 9 inda farar hula miliyan 5 su ma su ka rasa ran su.

Yaƙin ya shafi kusan dukkan sassan duniya kama daga Amurka, Turai, Afurka, Daular Othman, Daular Rasha da sassan Asiya. Shi kuma yaƙin duniya na biyu da ya fara daga 1939-1945 ya tattara dukkan duniya kuma ya faro ne a sanadiyyar mamaye ƙasar Poland da marigayi shugaban Jamus Adolf Hitler ya yi. Birtaniya da Faransa sun ƙaddamar da yaƙi kan Jamus.

Yaƙin ya yi sanadiyyar mutuwar tsakanin mutum miliyan 70-85 kuma ya haɗa da ma’aikata miliyan 100 daga fiye da ƙasashe 30. Haƙiƙa wannan yaƙi da ya fi kowanne zubar da jinin jama’a ya shiga kundin tarihi zuwa yanzu don a nan ne a ka yi amfani da makamin ƙare dangi na NUKILIYA.

Rahotanni na tabbatar da har yanzu garuruwa biyu na Japan da a ka jefa makaman Hiroshima da Nagasaki ba su farfaɗo yadda ya kamata ba. An samu asarar farar hula tsakanin 129,000 zuwa 226,000.

Tun daga wannan lokaci duniya ta ƙara fahimtar illar makamin NUKILIYA kuma har zuwa yanzu shekara 77 da su ka wuce Allah ya kiyaye ba a sake amfani da miyagun makaman ba. A zahiri hakan ya sa wasu ƙasashe ke ta fafutukar sai sun mallaki irin waɗannan makamai don zama garkuwa a gare shi su ko kuma su samu damar razana ƙasashen da su ke son cimma wata manufa a cikinsu.

Yaƙin tekun Pasha da a ka yi duk da ya haɗa da ƙasashen taron dangi amma bai zama yaƙin duniya na uku ba. A gaskiya ya dace duniya ta tashi haiƙan wajen hana duk wani dalili da zai hargitsa duniyar gaba ɗaya. Kun ga yadda yanzu ma ƙasashe da dama ke fama da yaƙin basasa ko bijirewa gwamnati.

Ku duba yadda ’yan tawaye su ka hana Somaliya zaman lafiya, ku duba yadda yaƙin basasa ya jefa Yaman cikin matsala tun 2014 har yanzu asarar rayuka a ka yi tsakanin sojojin gwamnati da na ’yan tawayen houthi, ku duba yadda ’yan Boko Haram su ka addabi ƙasashen yankin tafkin Chadi ga kuma ƙalubale na varayin daji a yankin Arewa maso yammaci da arewa ta tsakiyar Nijeriya.

Yaya ma a ka samu Afghanistan ta samu sararawar kasahe-kashe na tsawon shekaru da Allah ya ƙaddara ’yan Taliban za su dawo karagar mulki. Ga nan wasu ƙasashen Afirka sun kama samun zaman mulkin dimokuraɗiyya.

Ga batun DA’ESH, ga rashin adalcin manyan ƙasashe kan ƙanana tamkar a na zaman kashin dankali. Yau wane hali a ke ciki? Batun mamaye Ukraine da Rasha ke yi inda tuni hakan ya tava zamantakewa da tattalin arzikin duniya.

Na ji shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari na kawo batun yaƙin Ukraine na shafar tattalin arzikin duniya a lokacin da ya ke jawabin gabatar da kasafin kuɗin baɗi. Ba ma shi kaɗai ba shugabannin manyan ƙasashjen duniya ma na buga misali matsalolin duniya da alaƙanta hakan da yaƙi a Ukraine.

Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya ma Antonio Guterres ya maida hankali a batun yaqin na Ukraine don haka kusan duk lokacin da zai yi magana a yanzu sai ka ji ya kawo batun na Ukraine. Tsadar kaya yanzu musamman na masarufi an alaƙanta shi da yaƙi a Ukraine. Kasancewar Ukraine na fitar da hatsi mai ɗimbin yawa zuwa wasu kasashe don sayarwa, yaƙin ya sa fargabar tashin kayan abinci.

Hakan ma na faruwa ne a yanzu da Allah ya sa yaƙin bai gama ƙazanta ba har wasu ƙasashe su ka shigo kai tsaye ba, ya na da kyau a san yadda za a yi a yaiyafawa wutar da ta ke ruruwa ruwa don samun sa’idar dangin bani adama gaba ɗaya. Haƙiƙa akwai fitinar da za ta iya faruwa har ta yi sauƙi amma ba za ta ɗauki hankalin duniya ba.

Irin wannan kan shafi ƙasashe masu tasowa ne ko marar sa galihu inda za a riƙa bayanin za a turo mu su taimako ka ga a na ta zubar da jini ta hanya mai ban mamaki kuma ba wani fitaccen dalili don haka a ke ta raɗe-raɗin hayaƙi ba ya tashi inda ba wuta, hakanan wuta mai ruruwa a maƙera na buƙatar taimakon zuga-zugi.

A ido ga dai fitina a nan tsakanin mutanen da ba mamaki ba ’yan ƙabila ɗaya ne ko ma addini ɗaya amma fitinar ta ƙi ci ta ƙi cinyewa. Me zai sa wasu su riƙa kwantar da ’yan uwan su sun a yankawa kamar yankan rago, me ya sa wasu za su ɗauki mota cike da boma-bomai su ribzawa wani gini ko kuma wasu su ɗaura damarar bom su shiga jama’a don kashe waɗanda ba su yi mu su laifin komai ba?

Haƙiƙa ko ba a shigar da ƙasashen duniya kai tsaye a yaƙin Ukraine ba, to sun shiga a kaikaice don yadda hakan ke shafar tattalin arziki. Ko dai irin yaƙin duniya na yanzu na tattalin arziki ne inda wasu na zaune a garuruwan su amma talauci da yunwa sai ta gama da su ba tare da an yi ta’aziyya ko jaje a Majalisar Ɗinkin Duniya ba.

In sabon zamani haka ya sauya yaƙin zuwa na yunwa bayan na cacar baki da ya biyo bayan yaƙin duniya na biyu tsakanin ƙasashe masu ƙarfin makamai, to tuni an shiga yaƙin duniya na uku! Yanzu mutane na wa ke kwana da yunwa a Yaman, Somaliya, wasu yankunan Nijeriya ko mutum na wa su ka afka fatara a Lebanon har ya kai ga sai an yi zanga-zanga ko tafiya da bindigar roba kafin samun cirar kuɗi a ma’ajiyar mutum ta banki, wasu ma na buƙatar kuɗin don biyan kuɗin maganin cutuka masu tsanani ko biyawa yara kuɗin makaranta ko ma don sayen tattasai da tumatur.

A Lebanon hatta sojojin ƙasar na buƙatar abinci da magunguna don yadda ƙasar ta afka yaƙin duniyar karayar tattalin arziki da a ka daɗe ba a ga irin sa ba a tarihi.

Yadda yaƙin Ukraine ke sauyawa kwanan nan zuwa matuƙar zubar da jini da ramuwa da ƙarfin makamai na nuna buƙatar taka birki da janye muradun masu muradin cimma wata manufa. Gaskiya in a ka sake barazanar da shugaba Vladimir Putin ya yi ta fito da makaman ƙare dangi a wannan yaƙi to duk duniya sai ta girgiza.

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi gargaɗin cewa martanin ƙasar sa ga hare-haren da ya zayyana da na ta’addanci daga Ukraine zai yi munin gaske. Putin na magana ne gabanin taro na majalisar tsaron sa kan harin da Ukraine ta kai kan gagarumar gadar da ta haɗe Rasha da yankin Crimea, wacce Rasha kan yi amfani da ita wajen kai wa sojojin ta kayan aiki a fagen yaƙi.

Duk da haka ma Putin ya ce tuni Rasha ta kai hare-haren ramuwar gayya kan sassan makamashin soja da cibiyoyin sadarwa na Ukraine. Tun sanyin safiyar litinin makamai masu linzami na Rasha su ka yi ta dira a kan babban birnin Ukraine wato Kyiv da birane daban-daban a cikin Ukraine ɗin.

Shugaban Turkiyya Raceb Tayyib Erdoan na ƙarfafa ganawa da shugaban Rasha Vladimir Putin a babban birnin Kazakh wato Astana. Wannan cigaba da yunƙuri ne na Erdoan na neman sulhunta Putin da shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy don kawo ƙarshen fafatawa da a ke yi.

Shugaba Erdoan ya yi ƙoƙarin sanya Turkiyya ta zama ba ta da ɓangare a duk yaqin da ke afkuwa a tsakanin Rasha da Ukraine kuma ta na da alaƙa da dukkan ƙasashen biyu.

Dama Erdoan ya gana da Putin a Uzbekistan a watan jiya cikin shirye-shiryen gudanar da taron yankin su da zai duba fitinar da ta ɓarke.

Raceb Erdoan dai bai yi magana kan hare-haren da Rasha ta zafafa kan Ukraine ba da hakan a ta bakin hukumomin Ukraine ya yi sanadiyyar mutuwar kimanin mutum 19 da raunata 100.

Duk da haka an samu labarin ministan wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya yi magana ta wayar tarho da takwaran sa na Ukraine Dmytro Kuleba bayan hare-haren. Shugabannin Saudiyya da na Daular Larabawa ma na yunƙurin sa baki don dakatar da cigaban wannan fitina.

Saudiyya ta bayyana cewa ta na ɗaukar matakan daidaitar farashin man fetur ne ba wai ta na goyon bayan ƙasar Rasha ba ne kan muradun sauran ƙasashe.

Ƙaramin ministan wajen Saudiyya Adel Aljubeir ya bayyana haka a zantawarsa da Becky Anderson ta gidan talabijin na CNN.

Aljubeir ya ce umurnin rage haƙo ganga miliyan 2 ga manyan qasashe masu arzikin fetur da ƙungiyar ƙasahen OPEC ta yi, don amfanin masu amfana da fetur ɗin ne da kuma masu haƙo shi.

Ministocin makamashi na ƙasashen sun amince da wannan ragi da zai fara aiki a wata mai zuwa.

Haƙiƙa rage haƙo fetur ɗin zai tada farashin gangar fetur a kasuwar duniya.

Kammalawa;

Ya kamata duniya ta yi wuf ta shiga tsakani ta hanyar fasa dalilan da su ka haddasa Rasha ke marmarin mamaye Ukraine. Yaƙin ba zai yi wa kowa riba ba in am bar muradun ƙashin kai sun shallake muradun zaman jama’ar duniya lafiya.