Garƙame kafofin yaɗa labarai: BON ta yi tir da matakin Matawalle

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Kula da Kafafen Yaɗa Labarai ta Nijeriya (BON), ta nuna kaɗuwarta da kuma Allah wadai da matakin da Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya ɗauka na garƙame wasu kafofin yaɗa labarai huɗu mallakar gwamnati da masu zaman kansu a jihar.

Cikin sanarwar da ta fitar a ranar Lahadi mai ɗauke da sa hannun Sakatarenta, Dr. Yemisi Bamgbose, kuma a matsayin martani ga matakin na Matawallen ya ɗauka, BON ta ce a dokance Gwamnan ba shi da ikon da zai ba da umarnin rufe kafafen, kuma hakan da ya yi tamkar cin mutunci ne da kuma yin amfani da ƙarfin iko a inda bai dace ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa, BON kaɗai ke da ikon ƙwace lasisin gudanarwa na duk wata tashar rediyo ko talabijin da ta aikata ba daidai ba kamar yadda doka ta sahale mata.

Kazalika, sanarwar ta ce idan har ya kama a ƙwace lasisin wata tashar, nan ma ba da ka za a aiwatar ba dole sai an bi matakan da doka ta shimfiɗa.

Bugu da ƙari, BON ta ce rufe kafafen da Matawallen ya yi hakan ya saɓa wa Dokar Zaɓe ta 2022 wanda akwai buƙatar a taka masa burki da gaggawa tun kafin ya yi wa dimokuraɗiyyar ƙasar nan illa.

Daga nan, BON ta yi kira ga Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, Baba Alkali, da ya duba ya bai wa ɗaukacin kafafen yaɗa labarai da ke Jihar Zamafara tsaro domin kare su daga sharrin ‘yan bangar siyasa.

Hukumar ta kuma buƙaci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), da ta tabbatar da Gwamnan ya ɗanɗani kuɗarsa na rashin martaba sabuwar Dokar Zaɓe, sannan Gwamnatin Tarayya ta tura ‘yan sanda don sake buɗe kafafen da lamarin ya shafa.

Manhaja ta rawaito a ranar Lahadi, Gwamna Matawalle ya ba da umarnin gaggawa kan a rufe wasu kafafen yaɗa labarai guda huɗu a jihar bisa zargin yaɗa taron Jam’iyyar PDP wanda ɗan takarar gwamnan jihar a ƙarƙashin jam’iyyar, Dauda Lawal ya gudanar a ranar Asabar.