Za a iya ɗaukar shekaru kafin a shawo kan matsalar ‘yan bindiga – Sarkin Musulmi

Daga Umar Garba a Katsina

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya ce za a iya ɗaukar tsawon shekaru kafin a shawo kan matsalar ‘yan bindiga da ta addabi yankin arewa maso yammacin ƙasar nan.

Sarkin Musulmi ya bayyana haka ne a yau Litininin, wajen babban taron haɗin gwiwa wanda gwamnonin Jihohin arewa maso yamma haɗin gwiwa da hukumar jinƙai ta majalisar ɗinkin duniya (UNDP) suka shirya a jihar Katsina don inganta yanayin tsaro a jihohin yankin.

“Abin da ya kamata mu yi shi ne ƙalubalantar waɗannan ‘yan bindiga saboda mun san irin illar ‘yan ta da ƙayar baya ga rayuwarmu. Sai dai za a shafe tsawon shekaru kafin a magance matsalar gaba ɗaya,” in ji shi.

Ya cigaba da cewa sarakunan gargajiya a shirye suke domin haɗa gwiwa da jami’an tsaro da kuma gwamnoni bakwai na yankin domin ceto shi daga ɗimbin matsaloli da yake fuskanta.

Alhaji Sa’ad ya kuma ce, ya yi imanin za a iya samun hanyoyin rage barazanar da ‘yan bindigar ke da shi domin mutane su koma rayuwa ba tare da fargaba ba da kuma gudanar da harkokin kasuwanci.

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Kashim Shettima shi ne ya buɗe babban taron.

Taron zai tattauna ne kan hanyoyin da za a bi domin kawo ƙarshen matsalar tsaro da yankin na Arewa maso yamma ke fama dashi.

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin arewa maso yamma shi ne ya karɓi bakuncin taron.

Taron ya samu halartar mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, wanda ya wakilci shugaba Bola Tinubu, da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, gwamnoni bakwai na Jihohin arewa maso yamma, shugabannin hafsoshin tsaro da kuma sufeton ‘yan sanda, sarakunan gargajiya da dai sauran masu ruwa da tsaki.

Leave a Reply