Zan ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotu na soke takara ta – Binani

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohuwar ‘yar takarar kujerar gwamna ƙarƙashin Jam’iyyar APC a Jihar Adamawa, Sanata Aisha Dahiru Binani, ta sha alwashin ɗaukaka ƙarar hukuncin kotu da ta soke nasarar da ta samu a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar.

A wata tattaunawa da Binanin ta yi da wata kafar yaɗa labarai mai suna Muryar Arewa a jihar, ta ce Nuhu Ribadu kamar ɗan uwa yake gareta kuma yana da damar ƙalubalantar nasararta a kotu.

Binani ta ce ta ɗauki hukuncin na kotu a matsayin ƙaddara saboda a cewarta Allah ne ke ba da mulki ga wanda ya so.

Ta buƙaci magoya bayanta da cewa kada su lalata katunansu na zaɓe saboda hukuncin kotu domin za ta ɗaukaka ƙara.

“A matsayina na kodinetar kwamaitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a Jihar Adamawa, zan tabbatar da samun nasararta a zaɓukan 2023 da ke tafe,” inji Binani.

Idan za a iya tunawa dai, a ranar Juma’a da ta gabata ne wata babbar kotu mai lamba 1 da ke Yola, da mai Shari’a Abdulaziz Anka ke jagoranta, ta ayyana soke zaven fidda gwanin gwamna na Jam’iyyar APC a jihar ta Adamawa saboda cewa jam’iyyar ba ta bi ƙa’idoji da kuma sharuɗa da aka gindaya mata ba yayin gudanar da zaɓukan fidda gwani.

Mai shari’a Anka ya kuma gargaɗi Binani da cewa ta daina ɗaukar kanta a matsayin ‘yar takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar.