Jakadan Sin dake Nijeriya ya gana da shugaban jam’iyyar mai mulkin ƙasar Abdullahi Adamu

Daga CMG HAUSA

Kwanan baya, jakadan ƙasar Sin dake Nijeriya Cui Jianchun, ya gana da shugaban jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar Sanata Abdullahi Adamu.

A yayin ganawar, Cui Jianchun ya bayyana cewa, babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin karo na 20, wani muhimmin lamari ne a tarihin harkokin siyasar jam’iyyar da jama’ar ƙasar Sin.

A cikin shekaru kusan 10 da suka gabata, ƙarƙashin jagorancin jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin, ƙasar Sin ta cimma nasarar gina al’umma mai matsakaicin wadata daga dukkan fannoni, kuma ta samu sakamako mai kyau wajen kawar da talauci, da yaki da cin hanci da rashawa yadda ya kamata, da yaƙi da annobar COVID-19 da dai sauransu.

Ya ce jam’iyyar Kwaminis ta ƙasar Sin tana son zurfafa musanyar fasahohin da ta samu a harkokin mulkin ƙasa tare da jam’iyyar APC, da sa kaimi ga haƙiƙanin haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu, da kiyaye daidaito da adalci a duniya tare, da hada ƙarfi don gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga Sin da Afirka a cikin sabon zamani.

A nasa ɓangaren, Sanata Adamu ya taya murnar gudanar da babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin karo na 20 cikin nasara, ya kuma yaba wa mu’amalar dake tsakanin jam’iyyun biyu, da dangantakar dake tsakanin ƙasashen biyu, ya kuma jaddada cewa, ƙasarsa tana tsayawa tsayin daka kan manufar ƙasar Sin ɗaya tak a duniya.

Baya ga haka, ya bayyana aniyarsa ta ƙara koyo daga fasahohin da jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin ta samu wajen cimma nasara, da tabbatar da sabon ra’ayin bai ɗaya da shugabannin ƙasashen biyu suka cimma, da inganta haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu a fannoni daban daban, don ci gaba da samun sabbin nasarori, ta yadda jama’ar ƙasashen biyu za su amfana.

Mai fassara: Bilkisu Xin