Juncao, ciyawar da ke Rungumar makomar ɗan Adam ta bai ɗaya

Daga LUBABATU LEI

Jama, ko kun taba jin sunan Juncao? Wannan wata nau’in ciyawa ce da ake iya amfani da ita wurin noman laimar kwaɗo da ake iya mai da ita abinci ko magani, wadda ake kiranta ciyawar ƙasar Sin ko ciyawar samar da arziki a ƙasashe da dama.

A shekarun 1980, noman laimar kwaɗo ya zama muhimmin aiki da manoma ke dogara a kai wajen sauƙaƙa fatara a lardin Fujian da ke Kudu maso gabashin ƙasar Sin. Sai dai hakan ya haifar da matsala a sakamakon yadda manoma suke yawan saran bishiyoyi don yin amfani da su wajen noman laimar kwaɗo.

Ganin haka ya sa Mr. Lin Zhanxi, ƙwararren masanin ilmin noma da dazuzzuka na ƙasar Sin, da abokan aikinsa, suka yi ƙoƙarin nazari tare da gano fasahar noman laimar kwaɗo ta amfani da nau’in ciyayin Juncao a maimakon katako, a wani ƙoƙari na daidaita matsalar. Ta hakan, yawan dazuzzukan da ake sara domin noman laimar kwaɗo ya ragu da yawan gaske.

Baya ga haka, sakamakon yadda ciyayin Juncao suka kasance masu iya jure yanayi mai wahala, wadanda kuma suke da saiwoyi masu ƙarfi, baya ga kuma yadda suka kasance masu gina jiki, ya sa bayan noman laimar kwaɗo, ana kuma amfani da su wajen magance iska, da kwararowar hamada, da kuma kiwon dabbobi, wato ke nan, ciyayin na iya taka muhimmiyar rawa wajen raya tattalin arziki da kuma kiyaye muhalli duka.

Daga nan, sai Lin Zhanxi ya yayata fasahar zuwa gundumomi 506 na faɗin ƙasar Sin, fasahar da ta taimaka wajen buɗe ƙofar samun arziki ga al’umma da ke fama da talauci a ƙasar. A bara, akwai wani wasan kwaikwayon talabijin da ya yi matuƙar samun farin jini a ƙasar Sin, wanda ya bayyana yadda malami Lin Zhanxi ya yayata fasahar Juncao daga Fujian har zuwa yankin Xihaigu na jihar Ningxia, da ke Arewa maso yammacin kasar Sin, ta yadda manoman yankin suka sauƙaƙa fatara ta hanyar noman laimar kwaɗo.

Malami Lin Zhanxi bai tsaya a gida ba, a maimakon haka, ya ƙara yayata fasahar zuwa sauran ƙasashe da shiyyoyin duniya 106. A Lesotho, ya kafa tsarin noma da ke iya samar da laimar kwaɗo da nauyinsu ya kai ton 1.2 a kan faɗin ƙasa da bai wuce muraba’in mita 10 kacal ba, matakin da ya zama muhimmiyar kafar samun karin kudi shiga ga manoman wurin.

A ƙasar Rwanda, kwamitin kula da ayyukan gona na ƙasar ya yayata fasahar Juncao a sassan ƙasar wajen kare matsalar lalacewar gonakin ƙasar. Lallai, ciyayin Juncao sun zama ciyayin samar da arziki da alheri ga al’ummar ƙasashe masu tasowa da dama.

Daga ranar 16 zuwa 22 ga wata, an gudanar da babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis dake kan karagar mulkin ƙasar Sin karo na 20 a birnin Beijing, kuma Malami Lin Zhanxi ma ya halarci taron a matsayin ɗaya daga cikin wakilai 2296 na jam’iyyar. A yayin da yake halartar taron, ya kuma kiyaye tuntuba da abokan aikinsa. Wani lokaci, ya kan kuma tashi da tsakan dare, don yin musayar ra’ayoyi tare da takwarorinsa na ƙasashen Afirka da Latin Amurka.

Rahoton da shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya gabatar a gun taron na wakilan jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin karo na 20, ya yi nuni da cewa, “Kullum ƙasar Sin na nacewa ga bin manufar diplomasiyya, ta kiyaye zaman lafiyar duniya da tabbatar da samun ci gaban juna, don rungumar makomar dan Adam ta bai daɗa.

“Ƙasar Sin za ta ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙasashe masu tasowa bisa sahihanci da gaskiya, don kiyaye moriyarsu ta bai ɗaya”.

A game da wannan, malami Lin Zhanxi ya bayyana cewa, “Ƙasar Sin na samar da gudummawar fasahohinta a fannin ayyukan gona ba tare da gindaya wani sharadi ba, kuma muna samar da sahihiyar gudummawarmu, don fatan ganin an saukaka fatara.”

A shekarar 2020, ƙasar Sin ta cimma nasarar fitar da al’umma kusan miliyan 100 a karkarar ƙasar Sin daga ƙangin talauci, kuma kasancewarta ƙasa mai tasowa mafi girma a duniya, ba ta manta da sauran ƙasashe masu tasowa ba, har ma ta raba musu fasahohinta ba tare da ɓoye komai ba, don rungumar makomar ɗan Adam ta bai ɗaya.

Mai Zane: Mustapha Bulama