An rufe babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin na 20

Daga CMG HAUSA

Yau Asabar aka rufe babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin (JKS) na 20 a birnin Beijing. A yayin bikin rufe taron, wakilai 2338 mahalarta taron sun zabi kwamitin ƙolin jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin karo na 20, da kwamitin ladabtarwa da sanya ido na kwamitin ƙolin.

Kana an zartas da ƙuduri game da rahoton kwamitin ƙolin jam’iyyar JKS karo na 19, da ƙuduri game da rahoton ayyukan kwamitin ladabtarwa da sanya ido na kwamitin ƙolin karo na 19, da kuma ƙuduri kan gyararren kundin ƙa’idojin jam’iyyar.

Taron ya amince da shigar da sabbin nasarorin nazari kan tunanin shugaba Xi Jinping game da tsarin gurguzu mai halayyar musamman ta ƙasar Sin a sabon zamani da ake ciki tun bayan babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin karo na 19 a cikin kundin ƙa’idojin jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin.

Kuma bisa ga manyan ayyukan da jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin ta sanya gaba a babban taron wakilan JKS karo na 20, an daidaita tare da kyautata bayani kan burin da ake fatan cimmawa a kundin ƙa’idojin jam’iyyar. An kuma tabbatar da babban burin bunƙasuwar tattalin arziki da zamantakewar al’ummar ƙasar Sin, wato za mu cimma nasarar zamanantar da ƙasar Sin mai bin tsarin gurguzu nan da shekarar 2035, da gina ƙasar Sin ta yadda za ta zama kasa mai ƙarfi dake bin tsarin gurguzu na zamani nan zuwa tsakiyar wannan ƙarni, wato yayin cika shekaru 100 da kafa jamhuriyar Jama’ar Sin.

Xi Jinping ya shugabanci bikin rufe babban taro, tare kuma da gabatar da jawabi. Inda ya jaddada cewa, jam’iyyar kwaminisanci ta ƙasar Sin ta shafe shekaru ɗari na gwagwarmaya, kuma ta ɓullo da wata sabuwar hanya domin daukar jarrabawar.

Jam’iyyar tana da cikakken ƙwarin gwiwa da ƙarfin samar da sabbin mu’ujizai da za su burge duniya a sabon zamani. Ya kuma yi kira ga daukacin jam’iyyar da ta jagoranci al’ummomin dukkan ƙabilun ƙasar da su haɗa kai don gina ƙasa mai bin tsarin gurguzu na zamani bisa a dukkan fannoni, da kuma sa ƙaimi ga farfaɗowar al’ummar ƙasar Sin a dukkan fannoni.

Mai fassara: Bilkisu Xin