Zuwa ga Gwamna Umar Namadi kan kula da inganci abincin Ramadan ba biliyan N4.8

Spread the love

Daga ABUBAKAR M TAHEER

Assalamu alaikum. Da fatan Mai Girma Gwamna na cikin ƙoshin lafiya. Allah ya karɓi ibadunmu ya sa mai lada muke yi.

Malam Umar Namadi, kamar yadda ake yi maka kirari da ka na kan daidai, ƙungiyoyi da al’ummar Musulmi sun zuba ido domin ganin wainar da ake toyawa a wajen rabon abinci azumin watan Ramadan, wanda aka ware masa Naira Bilyan 4.8.

Shirin cike yake da tarin matsaloli kama daga inganci abinci, rashin tsafta a wasu muhallan, sarrafa abinci, canja sunayen waɗanda ba ’yan mazaɓa ba ko gari a madadin masu rabon abinci da dai sauransu waɗanda na gani da idona na ke sanar maka ta wannan hanya.

Wannna ta sanya dole na ke kiran Gwamna Umar Namadi da ya gayyato ƙungiyoyin ’yan sa kai (CBOs) da su shigo cikin lamarin rabon abinci, domin tabbatar da adalci ga al’ummar Jigawa.

Mai Girma Gwamna, kuɗi sama da Naira biliyan huɗu fa ba wasa ba ne, kuma adalci shi ka rantse za ka yi wa al’ummar Jigawa. Kada kirarin da ake yi maka na ka na kan daidai ya rufe maka ido wajen kasa zaƙulo ɓarna, don a magance ta, wanda hakan ba ƙaramar illa yake da ita ga jama’ar da ka ke jagoranta ba.

Mun ga hotunan da suka fito daga maƙociyar jiharmu, Kano, wanda biyo bayan shigo da ƙungiyoyi ’yan sa kai, an samu inganci a shi kansa nau’in abinci da ma kanta tsaftar abincin, domin kula da lafiyar al’ummar jihar a wannnan watan mai alfarma.

Ka ɗauka Jihar Kano ta ninka Jigawa da kaso mai yawa, an ware Naira biliyan takwas na abincin da ake rabawa, duk wanda ya ga hotunan lallai abinci ya amsa sunansa. Abinci ne mai rai da motsi. Amma abin takaici a nan Jihar Jigawa, an ware sama da Naira bilyan huɗu, amma ni shaida ne, shinkafa ce jagob da ƙosai sai kunu ake rabawa.

Wani abin takaici, wasu hotuna na nuna rashin tsafta da ma ƙazantar yadda ake sarrafa abinci da ma yadda ake raba abincin, ga kuma uwa uba rashin inganci, wanda ni shaida ne daga wani garin ko wata mazaɓar daga cikin masu aikin abinci.

An san Mai girma Gwamna da ziyarar bazata, ya kamata ka fara, domin zaburar da waɗanda aka ɗora wa alhakin kula da rabon abinci sun gaza ta ɓangarori masu tarin yawa, wanda irina da wasunmu sun zuba ido, domin ganin wane irin ƙoƙari za ka yi kan lamarin.

A kwanan nan ka bijiro da shirin jin ra’ayi na Gwamnati da Jama’a. Wannan rubutun nawa cike yake da saƙo, wanda bai kamata ka yi shiru ba tare da ɗaukar matakin da ya dace ba.

A matsayina na ɗan jarida, cigaban Jihar Jigawa shine ya fi cancanta da mu fi ba wa muhimmanci a daidai wannnan lokaci.

Ina fatan Mai Girma Gwamna zai duba wannan koke nawa ya ɗauki matakin gaggawa, wanda hakan shine zai sake tabbatar mana lallai fa akan daidai yake.

Bissalam.
Abubakar M. Taheer, ɗan jarida ne da ke zaune a garin Haɗeja da ke Jihar Jigawa. Za a iya samun sa a adreshin imel [email protected]

By ukarofi