Ƙaramar Sallah: Rundunar ‘Yan Sandan ta sha alwashin ba da cikakken tsaro a Kano

Daga RABI’U SANUSI a Kano

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta yi alƙawarin samar da cikakken tsaro ga ɗaukacin jama’ar jihar da dukiyoyin su.

Tabbacin haka na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Kiyawa, ya fitar a madadin Muƙaddashin Kwamishinan ‘Yan Sanda, DCP Mu’azu U. Mohammed, zuwa ga al’ummar jihar baki ɗaya.

Kakakin rundunar ya ƙara da cewa, hukumar tana mai taya al’ummar Musulmi a faɗin jihar da kewaye murnar bikin Ƙaramar Sallah da zai gudana.

Rundunar ta shawarci al’ummar Kano da su ƙaurace wa ɗaukar dukkan wani abu da ka iya hadda yamutsi ko faɗawa komar hukuma yayin shagulgulan bikin Sallah.

“Muna masu gargaɗin jama’a a kowane irin yanayi su guji aikata nau’in laifin da zai kai ga haifar da tashin hankali ko rashin zaman lafiya, ko karya doka, duk wanda aka kama da laifin aikata hakan zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tana da,” in sanarwar.

Sanarwar ta kuma bayyana lambobin da za a yi amfani da su don isar da wani koke a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso: 08032419754, 08075391163, 09029292926, ko kuma 08123821575