Ƙarshen maha’inta ya zo – Saƙon Buhari na Kirsimetinsa na ƙarshe a matsayin Shugaban Ƙasa

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin ƙarshen maha’intar ƙasa ya zo, sannan ‘yan ƙasa za su ga alheri a 2023 da ma bayan nan.

Buhari ya bayyana haka ne cikin saƙon taya murnar Kirsimetin 2022 da ya isar wa ‘yan ƙasa.

Ya ce, “Saƙona na ƙarshe ke nan game da Kirsimeti a matsayin Shugaban Ƙasa. Nan da makonni 22 wannan gwamnatin za ta miƙa wa ta gaba ragamar mulki.

“Wannan wata dama ce da ya kamata mu nuna wa duniya cewa a shirye Nijeriya take ta ƙarfafa dimokuraɗiyyarta.

“A ci gaba da raya lumana da murnar da ake samu a wannan lokaci har zuwa sabuwar shekara zuwa kuma zaɓuɓbukan 2023 zuwa gaba da haka.

“Ina mai tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewar, waɗanda suka ƙudiri aniyar dagula zaman lafiyar ƙasar nan da haifar mata da fitina, ba su kai bantensu ba,” in ji Buhari.

Ya ƙara da cewa, “Kasarmu na da albarka ta jama’a da sauran arziki. Mu yaba arzikin da muke da shi a wannan lokaci, tare da fatan ɗimbin alhairai za su lulluɓe ƙasar nan gaba.”

Daga nan, Buhari ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su zaɓi shugabannin da a shirye suke su ɗora daga inda gwamnatinsa ta tsaya dangane da yi wa ƙasa aiki a zaɓe mai zuwa.