Ƙungiyar NUT ta karrama gwamna Raɗɗa

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina Mallam Dikko Umar Raɗɗa ya lashe kyautar karramawa ta ƙasa kan gyaran fannin Ilimi.

Gwamnan ya samu kyautar zinariya ta girmamawa kan ci gaban ilimi da jituwa da malamai daga ƙungiyar Malaman makaranta ta ƙasa (NUT), saboda gagarumin sauye-sauyen da gwamnatinsa ta kawo a ɓangaren ilimi da kuma kulawar da yake nunawa ga walwalar malamai.

An miƙa wannan karramawa ne a ranar Lahadi, yayin bikin Ranar Malamai ta Duniya ta shekarar 2025 da aka gudanar a Eagle Square, Abuja, ƙarƙashin taken “Sake Fassara Koyarwa a Matsayin Sana’ar Haɗin Kai.”

A jawabinsa bayan karɓar kyautar, Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa gwamnatinsa ta ware fiye da kashi 25 cikin 100 na kasafin kuɗin jihar a cikin shekaru biyu da suka gabata don fannin ilimi adadi mafi girma a tarihin jihar.

“Mun gudanar da ɗaukar malamai da ba a yi ba a wannan ƙasa, inda muka ɗauki sama da malamai 7,000 a lokaci guda,” in ji shi.

“Haka kuma muna gab da ƙaddamar da tallafin musamman ga malamai masu koyarwa a karkara domin ƙarfafa musu gwiwa da kuma mayar da hankali kan ci gaban ƙasa.”

Gwamna Raɗɗa ya ƙara da cewa ci gaban ilimi shi ne ci gaban makomar ƙasa, inda ya jaddada cewa “ba tare da malamai ba, babu al’umma, babu Katsina.”

Ya sadaukar da wannan karramawa ga dukkan malamai na Jihar Katsina, yana mai godiya da jajircewarsu wajen gina makomar yara da inganta rayuwar al’umma.

“A madadin gwamnatinmu, abokan aiki da ɗalibanmu, muna godiya ga ƙungiyar malaman Najeriya bisa haɗin kai da goyon bayan da suke ba mu,” in ji Gwamna Raɗɗa.

A jawabinsa na bude taron, Babban Sakatare na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Mista Abel Olumuyiwa Enitan, ya bayyana koyarwa ta haɗin kai a matsayin wata hanya da ake ƙara amfani da ita a duniya wajen inganta sakamakon karatu.

Ƙaramar Ministar Ilimi, Farfesa Suwaiba Ahmad, ta yi bayani kan matakan da gwamnatin tarayya ke ɗauka don ƙarfafa haɗin kai tsakanin malamai ta hanyar Manufar Ci Gaban Malamai ta ƙasa (2022), Tsarin horar da malamai a fannin fasahar sadarwa da ƙwarewa, da kuma kafa ƙungiyoyin koyarwa na haɗin kai a makarantu.

Shugaban ƙungiyar malaman Najeriya, Kwamared Audu Titus Amba, ya yaba wa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa ci gaba da tallafawa kyautar karramawar malamai da makarantun shugaban ƙasa, tare da godewa gwamnonin da ke mara wa malamai baya wajen bikin Ranar Malamai ta Duniya.

By ukarofi