Ƙungiyar Sakkwatawa, Kabawa da Zamfarawa na ƙara bunƙasa a Legas – Shugaban ƙungiyar

Daga DAUDA USMAN a Legas

Shugaban Ƙungiyar Al’ummar Sakkwatawa Kabawa da Zamfarawa mazauna Legas na shiyyar ƙaramar hukumar Ojoromi Ajegunle da ke cikin garin Legas, Alhaji Adamu Abubakar Ajegunle ya bayyana cewa, ƙungiyarsa ta ’yan asalin Sakkwato, kebbi da Zamfara mazauna legas na ƙara bunƙasa.

A halin yanzu wannan ƙungiyar ta su tana ƙara samun nasarori a wajen gudanar da ayyukanta tare da bunƙasa harkokin ƙungiyar a Legas da kewayanta gaba ɗaya.

Shugaban ƙungiyar na shiyyar ƙaramar hukumar Ojoromi a Legas, Alhaji Adamu Abubakar ya faɗi haka ne a lokacin da ya ke yin tsokaci bisa ga nasarori da ƙungiyar tasu ta samu a Legas jim kaɗan bayan kammala taronsu da waɗansu manyan ƙusoshin siyasar Legas waɗanda suka haɗa da ƙabilun Yarabawa da Hausawa da sauran makamantansu domin ɗaukar matakai na warware rikice-rikicen da su ke faruwa a lokacin da al’umma su ke gudanar da harkokin zaɓuka tare da nemo hanyoyin zaman lafiya a tsakanin al’umma a lokacin gudanar da zaɓuka masu zuwa na shekarar 2023.

Ya cigaba da cewa, a yanzu haka ma ƙungiyar tasu ta ƙara ɗaura ɗamara wajen kare dukkan nau’in guguwar siyasa daka iya tasowa ta tada hankulan al’ummarsa da sauran jama’a masu gudanar da harkokin zaɓen da ke zuwa, domin kare mutuncin mambobin ƙungiyarsa da ma kare mutuncin ƙasar nan a Legas da kewayanta gaba ɗaya.

Haka zalika, ya cigaba da yin kira ga mambobin ƙungiyar tasu da sauran al’ummar arewacin Nijeriya mazauna jihar Legas da kewayanta da su cigaba da haɗa kawunan junansu tare da zaman lafiya da sauran ƙabilun da su ke zaune da su a yankunan da su ke zaune da su a ciki da wajen Legas.

Sannan luma ya cigaba da jinjinawa shugaban ƙungiyar APC Arewa kwaminiti a Legas, Alhaji Sa’adu Yusif Dandare Gulma a cewarsa bisa ga jajircewarsa tare da ƙoƙarinsa na kare mutuncin mambobin ƙungiyarsa ta APC arewa kwaminiti a Legas tare da haɗa kawunan ’yan Arewa da sauran ƙabilu mazauna Legas gaba ɗaya.

Daga ƙarshe ya ce, ya yi wa al’ummar Arewacin Nijeriya fatan alheri dama al’ummar Nijeriya baki ɗaya a bisa ga nasarar samun man fetur a arewacin Nijeriya wanda shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da haƙo shi a Gwambe Bauchi a ƙarshen watannan da ya gabata, da fatan Allah ubangiji ya cigaba da zaunar da ƙasar nan lafiya.