Ƙungiyoyin tsofaffin ɗaliban Kwalejin Shari’a sun gudanar da taro a Kano

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano

Ƙungiyar tsofaffin Ɗalibai na Kwalejin Shari’a ta ‘Aminu Kano College of Islam and Legal Studies’ da aka fi sani da Legal sun gudanar babban taro a Kano.

Tsofafun ɗaliban fannin shara’a aji na 2007 ƙarƙashin shugabancin Malam Munnir Ibrahim Bala ne suka gudanar da taron.

Babban Mai Shara’a na ƙungiyar, Barista Saifulahi Alhassan Aliyu, ya bayyana a taron inda ya ce, su da suka kammala wannan makaranta a shekaru 17 da suka wuce sun yi taron ne don sada zumunci da taimakon juna musammam waɗanda Allah ya karɓi ransu a yi musu adu’a kuma a taimaka wa iyalansu.

Ya ce, to yanzu haka an samu damar haɗa wasu kuɗaɗe don tallafa wa iyalai da marayun waɗanda Allah ya karɓi ransa a cikin wannan ƙungiyar.

Ya ƙara da cewa, ƙungiyar na ƙoƙari wajen haɗe ƙungiyoyin tsofaffin ɗalibai waje ɗaya domin magana da murya ɗaya da kuma samun fahimtar juna a tsakanin ƙungiyoyin tsofaffin ɗaliban na AKCILS.

Hakazalika, shi ma shugaban ƙungiyar tsofaffin ɗaliban kwalejin shara’a ta Legal aji na 2011 Malam Nura Lawan Sayid, wanda aka fi sani da Yasayadi Rijiyar Lemo, ya ce wannan taro sun yi shi ne domin taimaka wa marayu da raunana a cikin wannan ƙungiya ta su domin yanzu haka akwai wani wanda za a yi masa aikin ido a cikinsu kuma ƙungiyar ta yi huɓɓasa wajen taimaka aikin idon.

Ya ce, kuma akwai abubuwa da dama na ɗinke-ɗinken sallah da sauran abubuwa da suke wa iyalan waɗanda suka rasu kamar bada tallafin jari da dai sauransu. Don haka ya yaba wa ɗaukacin ɗaliban wannan ƙungiya ta tsofaffin ɗalibai aji na 2011 musamam irin gudunmawar da Malam Sani Rogo Aikawa, ke yi da sauran tsofaffin ɗalibai ke yi don cigaban wannan ƙungiya. A ƙarshe, Malam Shamsu Musa Usman, wanda shi ne tsohon shugaban tsofaffin ɗalibai a sashen masu karatun nazarin zamantakewar ɗan adam a Legal, kuma jigo a ƙungiyar aji na shekara 2020, ya ce, su ma sun yi taro ne kamar yadda magabatansu tsofaffin ɗalibai ke yin taruka domin sada zumunci da taimakon junu, kuma sune maƙasudin wannan taro nasu da manufa ta zo ɗaya da sauran ƙungiyoyin makarantar AKCILS.

By ukarofi