‘Ƴan banga sun kashe mutum bisa ɓatar wayar da aka ganta daga baya a hannun ɗan mai ita

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A ranar Lahadi, 16 ga watan Yuni, 2024, wani matashi ɗan shekara 29 mai suna Joe Philip, wanda aka fi sani da Aboy, ya gamu da ajalinsa a hannun ‘yan ƙungiyar bijilante ta sa-kai mai suna ‘Anioma Security Watch Network’ a Agbor, Ƙaramar Hukumar Ika ta kudu a Jihar Delta, lamarin dai ya samo asali daga zargin satar ƙaramar wayar Nokia.

A cewar wani ganau, lamarin ya fara ne a lokacin da Joe Philip ya dawo daga cocin ya kunna janareta don shaƙatawa. Wata dattijuwa da ke cikin harabar gida ta nemi ya caja mata wayarta a ɗakinsa. Yayin da Filibus ya kwanta, ɗan matar ya ɗauki wayar ba tare da sanar da shi ba. An nemi wayar sama da ƙasa a lokacin da matar ta zo karɓar wayarta, inda Philip ya yi tayin saya mata wata, amma ta ƙi kuma ta yi barazanar koya masa darasi idan ba a dawo da ainihin wayarta ba.

Ta yi watsi da tayin Philip na samar da irin wannan wayar, matar ta kira jami’an tsaron yankin, Anioma Security Watch Network, inda suka zo suka fara kai masa duka, suna neman a dawo da wayar da ya ɓata. Duk da roƙon da shaidun suka yi, ’yan bangar sun cigaba da yi wa Filibus duka har sai da ya fita hayyacinsa, imda daga baya rai ya yi halinsa.

Da suka fahimci tsananin al’amarin, ‘yan bangar sun kai gawar Philip wanda bai amsa laifi ba zuwa ofishinsu da ke lamba 17 Gbenoba Street, Agbor, inda wasu mitanen gari suka lalata musu motar sintiri, har sai da jami’an ‘yan sandan Nijeriya da sojoji suka shiga lamarin. Daga nan ne ‘yan sandan suka kai gawar Philip zuwa ɗakin ajiye gawa a babban asibitin Agbor, tare da rakiyar ’yan uwa da abokan arziki.

A cikin wani yanayi mai ban tausayi, bayan ‘yan sa’o’i kaɗan, an gano wayar Nokia ɗin a hannun ɗan matar, wanda ya amsa ya lallaɓa ya ɗauka ne don kada ya tashi Philip daga barci.

Mahaifin marigayin da ke cikin alhini ya bayyana alhininsa da ɓacin ransa, inda ya bayyana cewa ya roƙi matar da ta yarda a saya mata sabon waya, amma ta dage a dawo da ainihin wayarta.

“Na roƙi matar da ta ba mu damar saya mata sabuwar waya, amma ta dage cewa lallai ita ainihin tata take so,” inji mahaifin.