2021: Shekarar garkuwa da ’yan makaranta da hare-haren ’yan bindiga

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Shekarar 2021 ba shekara ce mai daɗin tunawa ga miliyoyin ’yan Nijeriya ba, saboda irin abubuwa na tashin hankali, firgitarwa da taɓarɓarewar tsaro da suka faru a cikin shekarar. Wannan ba yana nufin kuma babu wani abu na farin ciki da ya faru a ƙasar ko a rayuwar wasu ’yan ƙasa da ba zai zama abin faranta rai idan sun tuna da shekarar 2021 ba. Amma dai ga akasarin ’yan Nijeriya ba a shiga shekarar da ƙafar dama ba.

Idan abin mu yi ɗan tsokaci ne ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru cikin shekarar tun daga watan Janairu zuwa watan Disamba mai ƙarewa, lallai babu shakka za mu ga cewa, abubuwa da dama sun faru musamman ga rayuwar ɗalibai ’yan makaranta da masu garkuwa da mutane don karɓar kuɗin fansa suka riƙa sacewa rukuni rukuni daga wannan makaranta zuwa waccan, azabtar da su a cikin dazuka, domin tilastawa gwamnati da iyayen yara su ba su miliyoyin Naira a matsayin kuɗin fansa.

Sai kuma irin yadda ’yan ta’addan daji, gyauron mayaƙan Boko Haram da ’yan ƙungiyar awaren IPOB masu neman ƙasar Biyafara suke ci gaba da haifar da rashin tsaro, kisan gilla, da ta’addanci kan ’yan Nijeriya da ba su ji ba, ba su gani ba. Abin da ya haifar da asarar ɗimbin rayuka, dukiyoyin jama’a da kadarorin gwamnati, gami da cigaba da fantsamar ’yan gudun Hijira.

Abin takaici ne jin irin yadda waɗannan fitintinu da suka addabi jihohin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas suka jefa rayuwar mata da qananan yara cikin tagayyara da wahalhalu iri-iri. Rahotanni sun yi nuni da yadda ’yan ta’adda suke shiga gari su rika yi wa duk wata mace da suka gani fyaɗe ko kisan wulaƙanci. Lallai wannan shekara ce mai cike da ƙunci da baƙin ciki.

Yawaitar ƙungiyoyin ’yan ta’adda masu ɗauke da makamai suna aikata manyan laifuka har kimanin 200 daga Arewa zuwa kudancin ƙasar nan a tsukin wannan lokaci, abin razanarwa ne ga tsaron ƙasar nan. A daidai lokacin da ƙalubalen tsaro ke cin ƙarfin ƙoƙarin da rundunonin tsaro ke yi ta sama da ta ƙasa, saboda abin da masana harkokin tsaro ke dangantawa da rashin wadatattun jami’an da za a baza dazuka da ƙauyuka su fatattaki gungu gungun ’yan bindiga, da kayan aiki na zamani ko ingantaccen horon da ya dace da yanayin da ’yan ta’adda ke amfani da shi.

A cikin wannan shekara ta 2021 ne aka aka samu yawaitar fashe-fashen gidajen yari, da suka koma cibiyoyin gyaran hali, har fiye da goma, adadin da aka ce ba a tava samu ba a tarihin ƙasar nan. Wannan ya haifar da fantsamar fursunoni da manyan masu aikata laifuka cikin jama’a, yayin da ƙalilan daga cikin su ne za a iya cewa, an mayar da su ko kuma sun mayar da kansu. Da dama an ɗora alhakin faruwar hakan kan lalacewar tsarin tafiyar da gidajen kurkuku da kuma ƙarancin jami’an da ke kula da fursunonin, da kuma rashin wadatattun kayan aiki na zamani.

Tsadar rayuwa, hauhawar farashin kayan masarufi, qarancin kuɗaɗe a hannun jama’a. Yajin aikin ƙungiyoyin ma’aikata, malaman jami’o’i, ma’aikatan lafiya da masu jinya. Rikice-rikicen ƙabilanci, da rigingimun manoma da makiyaya, sun haifar wa ’yan Nijeriya ƙunci mai yawa. Farashin Dala na daɗa yi wa darajar Naira nisa, yayin da manyan ’yan kasuwar ƙasar har ma da gwamnati ke juyawa harkokin cinikayya da ƙasar Sin da wasu qasashen Gabas ta Tsakiya masu ƙarfin tattalin arziƙi.

Cutar murar mashaqo ta COVID-19 ta ci gaba da gurgunta harkokin gwamnati da kiwon lafiya a Nijeriya, yayin da hukumomi da ke kula da yaƙi da cutar ke ikirarin cewa suna kashe maƙudan kuɗaɗe wajen yaƙi da yaɗuwar cutar. Sai ga shi daf da ƙarshen shekarar, an samu ɓullar wasu sabbin nau’o’in cutar biyu, Delta da Omicron, sun ƙara bayyana, inda suka ƙara haifar da koma baya a ƙoƙarin da gwamnati da jami’an lafiya ke yi. Yayin da masana harkokin lafiya ke cewa, babu abin ɗaga hankali game da cutar, amma a gefe guda jama’a na binne ’yan uwan su da wani adadi mai yawa, da ba a iya tantance musabbabin mutuwar su ba.

Wasu ’yan Nijeriya na bayyana cewa, abubuwan da suka riƙa faruwa a cikin wannan shekara ishara ce ake yi wa jama’a kuma darasi ne da ya kamata mutane su yi la’akari da shi, don gyara rayuwar su, canja salon yadda suke tafiyar da rayuwar su, tanadi da rage facaka da almubazzaranci, da kuma ɗaukar rayuwa a sannu.

Daga ɓangaren addini kuma, ’yan Nijeriya sun samu ƙarin ƙarfin imani da Allah Maɗaukakin Sarki, inda aka riqa addu’o’i da miqa al’amura zuwa ga Allah, cikin harkokin su na ibada da yanayin zamantakewa. Jama’a sun fitar da tsammanin ƙoƙarin gwamnati ko jami’an ta, zai kawo sauyi a rayuwar su, sai dai a miƙa wa Allah.

A yayin da muke yaba wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari kan ƙoƙarin da gwamnatin sa ta ke yi na inganta cigaban ƙasar nan, lallai muna qara kiran da ya mayar da hankali kan abubuwan da za su farfaɗo da walwalar ’yan ƙasa, tsaro da cigaban kasuwanci da tattalin arziki.

Tallafin kuɗi da rabon ƙananan jari da ake rabawa raunana da masu qaramin ƙarfi, yana da kyau kuma ya taimaka wajen taɓa rayuwar wasu da dama. Amma kuma samar da abubuwan cigaba na zahiri da zai yi maganin wasu matsaloli masu yawa, kamar farfaɗo da masana’antu da samar da ayyukan yi, inganta tsaro da bunƙasar lafiya da sauran su.

Kamar yadda yake ƙoƙarin ganin ya samar da abubuwan da nan gaba za a tuna da shi a matsayin wanda ya samar da ginshiqin cigaba da tsare mutuncin Nijeriya a idon duniya. Ya kamata kuma a waiwayi halin da talakawa, ’yan gudun Hijira, matasa, da ma’aikata ke ciki, don haka ne zai sa a yi kewar sa har bayan kammala mulkin sa.

Addu’ar mu ita ce, Allah ya sa shekara mai zuwa ta zama mai albarka, a samu sauƙin kasha-kashe da satar mutane, ko ma a daina baki ɗaya, a samu sauƙin farashin kayan masarufi, da inganta zaman lafiya da walwalar jama’a. A samu wadatar ayyukan yi, da raguwar vata gari a tituna da cikin jama’a. Kishin ƙasa ya dawo, haɗin kai da mutunta juna su dawo.

Allah ya ba mu lafiya baki ɗaya, ya sa shekarar 2022 ta zama shekarar arziki da wadata ga kowa.

By Editor