2023: Akwai yunƙurin kashe Atiku idan ya ziyarci Kudu maso Gabas – IPOB

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Haramtacciyar Ƙungiyar Masu Fafutukar Kafa Ƙasar Biyafara (IPOB) ta yi zargin cewa wasu ’yan siyasa na shirin kashe ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.

A wata sanarwa da Emma Powerful, mai magana da yawun ƙungiyar ’yan awaren ya fitar a ranar Lahadi, 5 ga watan Fabrairu, 2023, ya ce, an shirya makircin ne a yankin Kudu maso Gabas da nufin ɓata sunan ƙungiyar IPOB da kuma magoya bayan jam’iyyar LP da ke da tushe da shugabancin ɗan takararsu Peter Obi.

“Ana shirin kashe Atiku Abubakar a yankin Kudu maso Gabashin Nijeriya kuma da shirin laƙabawa IPOB ko kuma ƙungiyar Peter Obi”, in ji sanarwar.

Sanarwar ta yi ikirarin cewa makircin zai jefa al’ummar ƙasar cikin ruɗani kuma zai haifar da ɗaukar fansa kan ‘yan ƙabilar Ibo a dukkan sassan ƙasar.

Ta ce, “Za a kashe Ndigbo ba tare da tausayi ba, kuma za a lalata musu dukiyoyi. Hatta magoya bayan Peter Obi ba za su tsira a waɗannan wurare ba.”

Sanarwar ta kuma yi ikirarin cewa makircin ba kawai zai jefa al’ummar ƙasar cikin tashin hankali bane, amma zai kawo cikas ga zaɓen 2023 mai zuwa.

Ƙungiyar ’yan aware ta cikin sanarwar ta yi gargaɗi ga ɗaukacin ‘yan ƙabilar Ibo da magoya bayan jam’iyyar Labour a ƙasar. Sun kuma yi barazanar ambaton sunayen mutanen da ke da hannu a shirin idan ba su dakatar shirin nasu ba.

Kamar yadda jadawalin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP ya nuna, Atiku ne ya ratsa jihohin kudu maso gabas irin su Enugu da Abia a wannan makon domin gudanar da gangamin yaƙin neman zaɓe.

A baya Atiku ya bayyana cewa zai tattauna da ƙungiyar IPOB kan fafutukar kafa ƙasar Biyafara idan har aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa.