Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Sufeto Janar na ’Yan Sandan Nijeriya, Usman Baba Alƙali, ya bayyana cewa, babu wani gwamna da za a sake bari ya hana jam’iyyun siyasa na adawa gudanar da taro a jihohinsu.
IGP Baba ya yi wannan maganar ne ranar Laraba a taron jam’iyyun siyasa na 2022 a Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya.
Sufeto Janar ɗin, wanda ya samu wakilcin Dandaura Mustapha, Mataimakin Sufeto Janar na Hukumar ’Yan Sanda (DIG), ya ce, an umarci kwamishinonin jihohi da su tabbatar an bai wa kowane ɓangare damar gudanar da yaƙin neman zaɓe.
Baba ya ƙara da cewa, yayin da ya kamata a yaba wa wasu gwamnonin da suka ba jam’iyyun adawa damar gudanar da ayyukansu cikin walwala, akwai ƙorafe-ƙorafe kan wasu.
Abin takaici, wasu daga cikin gwamnonin ba sa taimakawa al’amuran wasu jam’iyyu. Ba su kafa harsashin baiwa sauran jam’iyyun siyasa damar yin yaƙin neman zaɓe ba,” inji shi.
“Wasu suna ƙoƙarin yin amfani da kamfen ɗin. Wasu ma suna ɗaukar nauyin ’yan daba su bi ’yan adawa, su cire allunan talla, cire fosta, su lalata ofisoshinsu. Muna sane kuma muna da cikakkun rahotanni.
“A bisa haka, Sufeto Janar ya umarci dukkanin kwamishinonin ’yan sanda da cewa ka da a bar wani gwamna mai ci ya hana wasu jam’iyyun siyasa gudanar da yaqin neman zaɓensu a lungu da saƙo na jihohinsu.
Wannan koyarwar ta fito fili a rubuce da kuma ta baki.
“An umurci kwamishinonin ’yan sanda da su kamo duk ’yan daba a ko ina suke, duk wanda ya ɗauki nauyinsu, za mu kama su, mu gurfanar da su a gaban kotu, wannan umarni ne ƙarara.”
Ya ce, duk kwamishinan ’yan sandan da bai bi wannan umarni ba, za a canja masa wurin aiki.