Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya bayyana cewa babu wata gamayyar siyasa da za ta iya kada Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Ya buƙaci ‘yan adawa da masu neman takara su haƙura da buri, su kuma goyon bayan gwamnatin da ke ci yanzu.
Da ya ke jawabi a taron shugabannin jam’iyyar APC na Kudu maso Gabas da aka gudanar a Abakaliki, Gwamna Nwifuru ya ce fitowar Tinubu a matsayin shugaban ƙasa a 2023 nufin Allah ne ba nufin dan Adam ba, kuma ya jaddada cewa babu wani kawance ko haɗakar ‘yan adawa da za ta iya hana nasarar Tinubu a 2027.
Ya yaba wa Tinubu bisa sauye-sauyen tattalin arzikin da ya ke yi, inda ya bayyana shi a matsayin jarumin shugaba mai ƙarfin zuciya da iya yanke shawara mai tsauri domin farfaɗo da ƙasa. Nwifuru ya roƙi ‘yan Nijeriya, musamman ‘yan Kudu maso Gabas, da su ci gaba da haƙuri tare da mara wa shugaban ƙasa baya.
