Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Aikin gayya wata tsohuwar al’ada ce da al’umma suka saba amfani da ita, don taimakon junansu a yayin da aka fuskanci wani babban aiki ko ƙalubale da ya ke buƙatar hannu da yawa, domin a samu sauƙin magance shi. Ko da ya ke har yanzu ba za a ce an daina ba, musamman a ƙauyuka, amma ba kasafai aka cika bai wa aikin gayya muhimmanci ba, saboda yadda haɗin kai da zumunci ya yi rauni a tsakanin jama’a, bambance-bambance da hidimomin rayuwa sun sa jama’a ba sa kallon kansu a matsayin al’umma mai manufa da buri iri ɗaya, an koma zaman ’yan marina, kowa da inda ya sa gaba.
Ba aikin gayya kaɗai ba a baya hatta cin abinci ma iyaye da kakannin mu tare suke haɗuwa su yi a ƙofar gida ko a zauren wani babban mutum da ake ganin kimarsa, ko kuma mai faɗa a ji a cikin layi ko anguwa. Irin wannan haɗin kai tsakanin magidanta yana ba da damar tattauna muhimman batutuwa da suka shafi harkokinsu na rayuwa, zamantakewa da tarbiyyar iyali. Kuma ana samun nasara mai yawa, saboda shawarwari da ake bai wa juna ko wani tallafi da ake buƙata.
Ayyukan gayya da jama’a kan shirya na haɗin gwiwa a gonaki, gyaran titi, aikin gini, gyaran magudanun ruwa da harkokin tsaro yana taimakawa a samu ci gaba sosai a ɓangaren inganta zaman lafiya da tattalin arziki da kiwon lafiya. Aikin da idan aka bar wa mutum ɗaya nauyin gudanar da shi ba zai yiwu cikin sauƙi ba, ko ba zai yi kyau yadda ake so ba, ko ma ba zai yiwu ba gaba ɗaya, cikin haɗin kai zai fi amfanar da kowa. Ko da kuwa ba da jiki aka yi aikin ba, shawara aka zauna aka yi, aka haɗa gudunmawa, don a samu wasu da za su yi aikin a biya su.
Yana da muhimmanci jama’a su riqa taimakawa junan su wajen magance wasu ƙalubale da suke ganin yana shafar su a matsayin su na mazauna wani yanki ko wata anguwa, ko wurin kasuwanci ko aiki da sauran mu’amaloli da ke haɗa jama’a. Ba daidai ba ne a ce jama’a su naɗe hannu suna jiran gwamnati ko wani mai hannu da shuni ko ɗan siyasa ya zo ya gyara musu wata matsala da take damun su, matuƙar za su iya shawo kanta da kansu, idan sun haɗa kai zai taimake su samun sauƙi da wuri a maimakon su jira har tsawon wani lokaci ana jiran jami’an gwamnati su zo su yi aikin.
Tashi tsaye don taimakawa kai da kai wani ɓangare ne na nuna kishin kai da kishin ƙasa, kuma wata hanya ce ta tunatar da mahukunta, inda suka gaza ko ake da buƙatar kulawarsu. Abin takaici ne ka ga a wata anguwa kan fanfo ko rijiyar burtsatse ya lalace amma an rasa wani da zai ba da gudunmawa a gyara ko al’ummar da suke amfana da wajen su haɗa kuɗi a canja wani, don a ci gaba da amfana da wajen. Haka matsalar tsaro da yanzu ta gallabi jama’a, musamman a jihohin Arewa, kafa ƙungiyoyi na ’yan banga ko matasa ’yan ƙato da gora yana taimakawa wajen samar da ƙwarya-ƙwaryar tsaro ko da ba yadda ake buƙata ba, kafin jami’an gwamnati su kawo ɗauki daga baya.
Lokaci zuwa lokaci a kan samu wasu jama’a ko ƙungiyoyi da ke ankarar da jama’a muhimmancin hakan, kuma har a samu waɗanda za su yi koyi da hakan. Kamar a lokacin masu zanga-zangar EndSARS a jihar Legas, lamarin ya kai ga sai da magidanta suka rika fita suna kwana a titi suna tsare anguwanninsu, saboda yadda vata gari suke fasa gidaje suna sata. A nan Arewa ma muna ganin alfanun da haɗin kan matasa ya kawo a jihohin Borno, Naija da Zamfara da wasu garuruwa masu fama da matsalar tsaro, inda suka kafa ƙungiyoyin mafarauta, ’yan banga da ’yan sa kai, da suke taimakawa jami’an tsaro wajen yaƙi da ’yan bindiga da masu aikata ta’addanci. Kuma jama’a da kansu sun ga alfanun hakan.
A ƙaramar hukumar Doguwa da ke Jihar Kano ma ina da labarin yadda wata ƙungiyar Musulmi da take tura mutanen ta babban asibitin garin suna ba da ayyukan jin ƙai, share share da ba da gudunmawar jini ga marasa lafiya, domin ci gaban garin da inganta lafiyar al’umma. Ba da jimawa ba ma gamayyar wasu ƙungiyoyin direbobi da mazauna ƙauyen Ganawuri a ƙaramar hukumar Riyom da ke Jihar Filato sun fito sun yi dafifi domin gyara wani sashi na babbar hanyar Jos zuwa Abuja da ya yi matuƙar lalacewa, domin a samu sauqin zirga-zirga a hanyar, ba tare da sun zauna jiran sai gwamnati ta zo da manyan motocin aiki an gyara ba.
Wani lokaci irin wannan aikin gayya ba wai yana maganin matsalar gaba ɗaya ba ne, amma yana rage ƙuncin da jama’a ke fuskanta da kuma samar da sauqin rayuwa ga jama’ar da ke wuri ko yankin da abin ke faruwa. Haɗin kai na da matuƙar muhimmanci, kuma ko da hukumomi sun fi sauraron koke-koken da aka yi a ƙungiyance, da ba da tallafin da ake nema, yadda kowa zai amfana.
A ƙungiyance ko a al’ummance jama’a za su iya duba wata matsala da suke ganin tana buƙatar tallafin gaggawa, domin a haɗa hannu a yi maganin ta, ba tare da ta tsananta har ta gallabi akasarin mazauna yankin ba. Matsaloli irin na yau da kullum da suka shafi harkar lafiya da tsaro, samar da ruwan sha, gyaran magudanun ruwa, gyaran makarantu, ɗaukar nauyin malamai da kula da marayu da zawarawa, duk wasu abubuwa ne da ya kamata jama’a su mayar da hankali a kan su ba sai wasu turawa daga wata ƙasa ko wata hukuma ta gwamnati ta kawo musu ɗauki ba.
Wani lokaci mutum zai yi takaicin yadda za ka ji muryoyin wasu mutane a kafafen watsa labarai suna zagin gwamnati ko ’yan siyasar yankin su kan wata matsala da su da kansu idan sun haɗa kai za su iya yin maganinta, ko kuma hakan ya ƙarfafa wa gwamnati ko wani mai hannu da shuni gwiwa ya shiga cikin aikin da na sa tallafin.
Lallai akwai buƙatar jama’a su rungumi salon yin aikin raya ƙasa da tallafawa ƙoƙarin da hukumomi ke yi na sauke nauyin da ke kansu, don faɗaɗa ayyukan cigaban al’umma. A lokaci guda kuma tunatarwa ce ga ’yan siyasa da wakilan al’umma su riqa sauraron koke-koken jama’a suna kai ziyarar gani da ido, don sanin irin tallafin da jama’a ke buƙata da inda za su sa hannu a samar da cigaban da jama’a ke nema a ƙarƙashin mulkin dimukraxiyya.
Yana da kyau jama’a su riƙa kafa kwamitoci na al’umma, waxanda za su ƙunshi ƙwararru da Allah ya hore musu daga cikin ’ya’yansu maza da mata, domin su riƙa kula da wasu muhimman ɓangarorin rayuwa da jama’a ke buƙatar sa hannun hukumomi, don samun inganta walwalar su da ta ’ya’yansu. Sannan su waxannan kwamitoci su riƙa fitar da manufofi da ajandoji da za su sa a gaba, mataki-mataki, suna bibiyar su, har a kai ga cimma ƙudirorin da ake neman samu. Waɗannan kwamitoci su za su riƙa bin sawun ma’aikatun gwamnati da wakilan siyasa na al’umma, domin nunar musu da abin da jama’ar da suka zave su ke buƙata.
Masu hikimar magana dai na cewa, hannu da yawa maganin ƙazamar miya! Allah ya ba mu shugabanni masu kishin jama’arsu da son cigaban yankunansu. Amin.
