NDLEA ta lalata kadada 255 na gonakin tabar wiwi a Ondo

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Mai magana da yawun Hukumar Yaƙi da Sha da Safarar Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), Femi Babafemi, ya bayyana cewa jami’an hukumar sun kama tare da lalata gonakin tabar wiwi da suka girman kadada 255 a tsakanin ƙananan hukumomi biyar na jihar Ondo.

Babafemi ya bayyana hakan ne cikin bayanan da ya wallafa a shafin Facebook na hukumar a ranar Laraba, inda ya ce ya ɗauki jami’an nasu mako guda suna aiki a yankin.

Kazalika, ya ce sun kama mutum 13 da ake zargi da noman tabar kana an gano irin tabar mai nauyin kilogiram 250 da kuma tabar mai nauyin 63.85kg a dazukan Omolowo/Powerline da Ipele da Ala da Ogbese da Utte da kuma dajin Okuluse.

Shugaban NDLEA na ƙasa, Brig. Gen. Mohamed Buba Marwa (Mai murabus), ya jinjina wa jami’an hukumar bisa wannan gagarumar nasarar da suka samu wanda ke nuni da ƙoƙarin da suke yi na cika umarnin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, da ya buƙaci hukumar ta shiga ta binciko tare da lalata gonakin da ake noman wiwi.

A ƙarshe, Marwa ya ƙarfafa wa jami’ansa gwiwa kan su ci gaba da nuna sadaukantaka da kuma jajircewa a bakin aiki yadda ya kamata.

By Editor