Benzema ya sake zura ƙwallaye uku a wasa ɗaya a Gasar Turai

Spread the love

Ƙwallayen da Karim Benzema ya ci wa Real Madrid ya basu damar doke Chelsea da ƙwallaye 3-1, nasarar da ta sanya masu riƙe da kofin gasar zakarun Turai shiga tsaka mai wuyar ficewa daga gasar zakarun Turai a matakin kusa da ƙarshe.

Benzema ne dai ya jefa dukkanin ƙwallaye ukun a ragar Chelsea, inda ya ci biyu kafin tafiya hutun rabin lokaci, ta uku kuma bayan dawowa daga hutun zangon farko na karawar da suka yi.

A ɓangaren Chelsea, Kai Havertz ne ya rage tazarar da aka samu da ƙwallo 1 tilo da ya ci wa ƙungiyar tasa. Wani abu da ya ɗauki hankali yayin wasan dai shi ne yadda golan Chelsea Edouard Mendy ya yi kuskuren da ya bai wa Benzema damar jefa ƙwallo ta uku a ragarsu.

Wannan ne karo na biyu da Benzema ya ci ƙwallaye uku cikin wasa guda, wato ‘hat-trick’ a turance, cikin gasar Kofin Zakarun Turai, bayan da shi kaɗai ya ci ƙwallayen uku a karawarsu da Paris Saint-Germain a wasa na biyu na zagayen da ya ƙunshi ƙungiyoyi a gasar Zakarun Turai.

Sai ranar 12 ga Afrilun nan Chelsea za ta yi tattaki zuwa birnin Madrid, domin sake karawa da abokiyar hamayyarta a karo na biyu.

Kofin gasar Zakarun Turai na ƙarshe da Real Madrid ta lashe shine na 13 a shekarar 2018.

By Editor