Sojoji sun ceto mutum 848 daga masu garkuwa, yayin da ‘yan ta’adda 1,158 suka miƙa wuya a Borno – Hedikwatar Tsaro

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA

Hedikwatar Tsaro ta Ƙasa (DHQ) ta ce, sojojin Nijeriya sun samu nasarar kuɓutar da mutane 848 da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su, kana sun kashe ‘yan ta’addan guda 85 sannan sun cafke 119, yayin da wasu ‘yan ta’addan sama da dubu 1,158 su da iyalansu suka mika wuya a tsawon shekaru uku da suka wuce a shiyyar Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.

Daraktan yaɗa labarai na hukumar tsaron, Manjo Janar, Benard Onyeuko, shi ne ya shaida hakan a ranar Alhamis yayin da ya ke bayyana nasarorin da sojojin suka samu zuwa yanzu, yana mai cewa, sojojin sun kuma kama wani mai suna Abdurrazaq Hudu, da ke safarar kayayyaki ga ‘yan ta’addan (ISWAP) a ƙauyen Mutum Biyu da ke Ƙaramar Hukumar Gassol a jihar Taraba.

General Onyeuko ya ce sun kama bindigogi ƙirar AK47 guda 49 a Arewa maso Gabas da alburusai samfurin 7.62mm guda 728, MG’s guda 4, bindiga ƙirar G3, 60mm mota guda 3, bindiga AA guda, SMG, grenade, UXO anti tank RPG bomb, bindigar gargajiya guda 11, bindiga ƙirar tripod da sauransu.

Ya ce da kayan da suka kama daga ‘yan ta’addan da waɗanda suka tuba da waɗanda kuma aka ceto duk an miƙa su ga hukumomin da suka dace domin ɗaukar matakan da suka kamata.

A Arewa maso Yamma kuwa, ya bayyana cewar sojojin da ke aiki a rundunar Hadarin Daji suna kan ƙoƙarin daƙile aniyar ‘yan ta’addan, inda suka ceto mata 32 da yara 18 a jihar Zamfara. Sa’anna kuma suka kashe ‘yan ta’addan da dama.

By Editor