Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Sama da al’ummar Musulmi 100 da waɗanda ba Musulmi ba ne suka amfana da wani shiri na musamman na raba kayayyakin abinci da kuɗaɗe ga ɗimbin mabuƙatan dake Lafiya, Babban Birnin Jihar Nasarawa.
Taron rabon kayayyakin wanda aka gudanar a fadar Maimartaba Sarkin Lafiya, Alhaji Sidi Bage ranar Talata 26 ga watan Afrilun shekarar 2022 da ake ciki, ya samu halarar Maimartaba Sarkin da manyan ‘yan siyasa da ƙungiyoyin addinai da malamai da sauransu.
Da yake jawabi jim kaɗan kafin a fara rabon kayayyaki da kuɗaɗen, shugaban kwamitin zakka wanda ya gudanar da rabon, Mai Shari’a Badamasi Maina (mai ritaya) ya faro ne da bayyana taƙaitaccen tarihin kwamitin wanda a cewarsa Mai martaba Sarkin Lafiya Alhaji Sidi Bage ne ya umurci a kafa shi kimanin shekara ɗaya da rabi da ta gabata da nufin nemo tare da tattara zakka daga masu hannu da shuni da ƙungiyoyi da masana’antu daban-daban don raba wa mabuƙata musamman a wannan lokacin azumi.
Ya ce jim kaɗan da kafa kwamitin sai shi da sauran mambobin kwamitin suka fara gudanar da aikin, inda suka yi ta tuntuɓar jama’a da wurae daban-daban inda suka tara zakkar suka kuma shirya taron rarraba su ga gajiyayyu cikin al’umma kamar yadda Maimarta Sarki ya buƙace su.
Ya kuma yaba wa Sarki Sidi Bage dangane da hangan nesa da ya yi na kafa kwamitin, inda ya sanar cewa bayan kafa kwamitin shi kansa sarkin ya kuma bada tasa zakka don amfanar mabuƙatan.
Daga nan sai ya yi alƙawari cewa kwamitin zai cigaba da faɗaɗa aikin nasa na neman zakka daga masu hannu da shuni da sarakunan gargajiya da ƙungiyoyi da sauransu don tabbatar an cimma kyakkyawar burin shirin, inda a ƙarshe ya sanar cewa bayan buhunan shinkafa da dawa da sauransu, kwamitin ya kuma tara tsabar kuɗi sama da Naira 450.
Tun farko a jawabinsa a matsayin baƙo na musamman a wajen taron, maimartaba Sarkin Lafiya, Mai shari’a Sidi Bage ya yaba wa kwamitin tara zakkar dangane da kyakkyawar aikin da ya gudanar.
Ya ce ba shakka kwamitin ya cancanci yabo idan aka yi la’akari da yadda ya iya tara waɗannan kayayyaki masu yawa da kuɗaɗen don raba wa mabuƙatu, inda ya buqace kwamitin ya cigaba da wannan namijin ƙoƙari.
Basaraken har ila yau ya yi amfani da damar inda ya yi kira na musamman ga masu hannu da shuni da ƙungiyoyi daban-daban da al’umma baki ɗaya su riƙa fitae da zakkar su musamman wa kwamitin don a cewarsa duk wanda ya yi haka ba shakka zai samu gagarumin lada tun anan duniya da lahira baki ɗaya.
Sannan ya kuma buqaci waɗanda suka amfana da tallafin na farkon su yi amfani da su yadda ya kamata, inda ya buƙaci waɗanda ba su samu ba su yi haƙuri nan gaba za su samu.
Abubuwa da aka gudanar a yayin taron sun haɗa da ƙaddamar tare da rabon kayayyaki da tsabar kuɗaɗen zakkar ga ɗimbin mabuƙata da dai sauransu.
