Shin an cimma manufofin rufe iyakoki a Nijeriya?

Spread the love

An ɗauki kimanin wasu ‘yan shekaru da iyakokin ƙasar nan ta ɓangaren Arewaci suke a garƙame, jim kaɗan bayan ɗaukar matakin yin hakan daga Shugaban ƙasa Mal. Muhammadu Buhari. A kuma makon da ya gabata ne, aka ga takardar sanarwar buɗe wasu daga cikin iyakokin da a da aka rufe su bisa dalilai kamar haka;

1- Don magance shigo da makamai zuwa ga ‘yan ta’adda.

2- Don havaka tattakin arzikin cikin gida, da rage dogaro da kayan ƙetare.

3- Don inganta noma da samar da abincin da zai ishe mu har mu baiwa maƙofta, da sauran wasu dalilai dai gasu nan barkatai.

To tambaya a nan, shin a cikin dalilan da suka tilasta garƙame bakin iyaƙoƙin an cimma nasarorinsu ne da a yanzu aka ga dacewar buɗe su? Misali, daga waccan lokacin zuwa yanzu Kamfanoni nawa aka samar?

Darajar kuɗin hada-hada ƙaruwa suka yi ko raguwa? Mun iya samar da adadin abincin da kan ishe mu har mu miƙawa maƙobta? Idan duk amsar ta zama a a, to don me za a buɗe a yanzu? Dama ƙeta ce kawai ta sanya aka doɗe su tun asali?

Daga Kwamared Sani Shehu Lere Kaduna, 08062798146

By Editor