Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya kuma ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana shirinsa na sake fasalin Nijeriya domin bunƙasa tattalin arzikin ƙasa da tsaro, idan har aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa.
Atiku, wanda ya bayyana haka a wata ganawa da ya yi da wakilan zave na jam’iyyar PDP a Lahadin makon nan a Abiya, ya ce zai kawo sauyi a ƙasar idan aka ba shi dama.
Ya ce indai ‘yan ƙasa suna so su cimma muradun su, akwai buƙatar jam’iyyar PDP ta samu nasara a zaɓen 2023.
Ɗan takarar ya ce takardarsa ta mayar da hankali ne kan muhimman abubuwa guda biyar da su ka haɗa da haɗin kan ƙasa, bunƙasa tattalin arziki, tsaron ƙasa, ilimi da kuma sake fasalin ƙasa.
“Tare za mu iya cimma dukkan waɗannan manufofin idan muka haɗa kai a jam’iyya,” inji shi.
Har ila yau, shugaban jam’iyyar PDP na jihar Abiya, Cif Asiforo Okere, ya bayyana cewa masu ruwa da tsaki sun ji daɗin karɓar ɗan takarar shugaban ƙasar.
Okere ya ce irin gudunmawar da ɗan takarar shugaban ƙasa ya bayar ga jam’iyyar ba za ta taɓa yin ƙasa a gwiwa ba.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya yi wa Atiku jagora ya kuma biya masa buƙatunsa na zama shugaban ƙasar Nijeriya.
