Masanin Nijeriya: Yadda Amurka da ƙasashen Yamma ke furta kalaman tsokana zai ƙara rashin zaman lafiyar duniya

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Wani masanin ƙasar Najeriya, Joseph Peter Ochogwu, ya bayyana a yayin hira da ‘yan jarida cewa, Amurka da ƙungiyar NATO, suna cigaba da neman tada jijiyar wuya, da yin fito-na-fito, da bayyana kalaman tsokana, game da rikincin Rasha da Ukraine. Lamarin da ke kara ta’azzara ƙaruwar rashin zaman lafiya.

Joseph Peter Ochogwu, farfesa ne a jami’ar Nile dake Najeriya, ya ce, NATO da ƙawayenta, suna kara haifar da tashin rikici, sannan tsadar farashin muhimmin kayan masarufi a duniya yana ƙara ƙamari, wanda hakan kadai yana iya yin sanadiyyar rashin zaman lafiya a sauye-sauyen fagen siyasar duniya.

Ochogwu ya bayyana farin cikinsa game da matsayar da ƙasar Sin ta ɗauka, wajen ƙoƙarin jan hankali don samun zaman lafiya, da ƙoƙarinta na daga matsayin neman hawa teburin tattaunawar sulhu game da rikicin tsakanin Rasha da Ukraine. Ya bayyana cewa, ƙasar Sin, ba kamar ƙasar Amurka da sauran ƙasashe ba ne, waɗanda ke yin kiraye-kirayen neman ƙaƙaba takunkumai, maimamon hakan, Sin ta zabi yin aiki tukuru, wajen neman maslaha don warware rikicin ta hanyar bin matakan siyasa kan batutuwan dake shafar rikicin Rasha da Ukraine. A bayyane take cewa, ƙasar Sin ta yanke shawara ba tare da dogaro kan kowa ba, game da matakan diflomasiyyarta.

Mai fassara: Ahmad

By Editor