Kamfanonin Amurka sun ci riba yayin da ake fama da wahalar hauhawar farashin abinci

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Abokaina, a wajenku, farashin kayayyakin abinci ya karu?

Yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine, da takunkuman da ƙasashen yamma suka ƙaƙaba wa Rasha, sun dakatar da cinikin takin zamanin da ake samarwa a ƙasashen Rasha da Belarus, lamarin da ya sa kuɗin da ake kashewa a aikin gona ya ƙaru. Baya ga wannan batu, yadda Ukraine da Rasha suka dakatar da aikin fitar da alkama da masara zuwa ƙasashen waje, sun sa farashin kayayyakin abinci na ƙasashe daban daban ya ƙaru sosai. Yanzu a ƙasar Masar, farashin burodi ya karu da kashi 50%. Yayin da a ƙasar Lebanon, farashin burodi guda ɗaya ya kai dalar Amurka 9.

Sa’an nan a ƙasar Senegal, ko da yake gwamnati ta ɗauki matakan daƙile hauhawar farashin kayayyaki, amma farashin burodi ya ci gaba da karuwa daga Cefa 150 zuwa Cefa 175, wato farashin ya ƙaru da kashi 16.6%.

Hauhawar farashin abinci wahala ce ga jama’a, amma duk da haka, akwai wanda ya ci riba sakamakon wannan matsala. Mun san wasu shahaharrun manyan kamfanoni 4 suna shawo kan kashi 80% na cinikin hatsin ƙasa da ƙasa, sa’an nan ƙasar Amurka ta mallaki 3 daga cikinsu, wato kamfanonin ADM, Bunge, da Cargill. Wadannan kamfanoni sun ci riba sosai bisa hauhawar farashin abincin da ake samu, inda kuɗin shigarsu ya ƙaru da kashi 53%, 80%, da 64%.

Yakin da Rasha da Ukraine suke yi ya sa dukkan kamfanonin hatsi da na samar da makamai na ƙasar Amurka cin riba sosai. Saboda haka, ba abin mamaki ba ne yadda ƙasar Amurka ba ta son ganin ƙarshen yaƙin, inda ta yi ta jigilar makamai zuwa Ukraine don tabbatar da samun daidaituwa tsakanin ƙarfin sojin kasashen 2, tare da tsai da ƙudurin “ yaki da ƙasar Rasha, har sai dukkan ‘yan ƙasar Ukraine sun mutu”.

Haƙiƙa su ma manyan kamfanonin cinikin hatsi na ƙasar Amurka sun dade suna ƙorafe-ƙorafe kan cewar, farashin kayayyakin abincin duniya bai yi tsada ba. Saboda haka sun yi ta matsawa gwamnatin ƙasar Amurka lamba, don neman habaka yin amfani da makamashin da aka samar daga hatsi. Zuwa shekarar 2021, hatsin da ƙasar Amurka ta sarrafa shi zuwa makamashi ya kai ton miliyan 170, wanda ya kai kashi 40% na dukkan hatsin da aka yi amfani da shi a ƙasar. Wadannan hatsi, idan an raba su ga al’ummomin duniya, za a iya ciyar da mutane miliyan 460 har tsawon shekara guda. Sai dai ƙasar Amurka ta kone su kawai a matsayin makamashi.

Tunanin kamfanonin ƙasar Amurka shi ne: Idan akwai ɗimbin hatsin da zai sanya dukkan mutanen duniya su ci su ƙoshi, to, a kone wasunsu a matsayin makamashi, har lokacin da wasu mutane sun fara fama da yunwa, ta yadda ake son ɗaga farashin hatsin. Wato kamfanonin ba za su so a sayar da hatsi a matsayin abinci ba, illa dai farashinsa ya ƙaru zuwa wani matsayin da zai gamsar da su ba. Ribar da kamfanonin Amurka suke samu na dogaro ne kan dimbin mutanen da suke fama da yunwa a sauran ƙasashe.

Ta haka za mu iya fahimtar cewa, moriyar ƙasar Amurka ta kan saba wa moriyar mutanen duniya: Idan ana fama da tashin hankali a sauran ƙasashe, kana mutanen kasashen suna shan wahala, to, kamfanonin ƙasar Amurka za su ci riba sosai, kana tattalin arizkin ƙasar ma zai karu cikin sauri. Idan farashin abinci ya ƙaru, ƙasar Amurka za ta iya sayar da hatsi don cin riba. Idan akwai matsalar ƙarancin makamashi, ƙasar za ta sayar da man fetur don samun kuɗi. Idan ana yaki, to, sai ta sayar da makamai don neman riba.

Idan wata ƙasa ta gamu da matsalar tattalin arizki, a kan janye kudin jari daga wannan ƙasa. Sa’an nan waɗannan jari ma su kan shiga cikin kasar Amurka, waɗanda suke wadatar da mutanen ƙasar. Wannan batu, a ganina, shi ne dalilin da ya sa ƙasar Amurka ke kokarin ta da zaune-tsaye da rikici a wurare daban daban na duniya.

Mai fassarawa: Bello Wang

By Editor