Zaɓen PDP: Wike ya fice daga zauren taro bayan da aka bayyana Atiku a matsayin wanda ya yi nasara

Spread the love

Daga WAKILINMU

Ɗan takarar Shugaban Kasa ƙarƙashin Jam’iyyar PDP, Gwamna Nyesom Wike, ya fice daga zuren da PDP ta gudanar da zaɓen fidda gwani a daidai lokacin da Alhaji Atiku Abubakar ke gabatar a jawabin amincewar nasarar da ya samu.

Alamu sun nuna Wike ya fice daga wajen zaɓen ne saboda rashin jin daɗin sakamakon zaɓen wanda Atiku ya samu nasara a kansa.

A ranar Asabar da ta gabata Jam’iyyar PDP ta gudanar da zaɓen fidda gwani a Babban Dilin Wasannin Motsa Jiki da ke Abuja don tsayar da ɗan takararta na Shugaban Ƙasa a zaɓen 2023.

Da yake jawabi jim kaɗan bayan tabbatar da shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen, Atiku ya lashi takobin yin aiki tukuru idan ya zama Shugaban Ƙasa wajen inganta haɗin kan ‘yan Nijeriya.

Ya ce, “A yau Mun sake kafa tarihi. Tarihin da muka yi amannar zai kawo canje-canje na alheri a ƙasa da ma tsarin dimokuradiyyarmu.”

Atiku ya jaddada cewa yaƙin neman zaɓensa zai ta’allaƙa ne a kan abubuwa biyar, ciki har da sha’anin tsaron ƙasa, haɗin kan ƙasa, tattalin arziki da suaransu.

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar ya samu nasarar lashe zaɓen ne da ƙuri’u 371, sai Wike da ke bi masa da ƙuri’u 237, yayin da Saraki ya zo na uku da ƙuri’u 70.

By Editor