Gangancin mahaya babur a titunan Nijeriya

Barazanar mahaya babur musamman ma ’yan acaɓa a kan manyan tituna a sassan Nijeriya na ƙara ɗaukar hankali. Baya ga tuƙin ganganci da kawo matsala ga sauran masu amfani da hanyar, sun kuma vullo da wani sabon salo na zama ’yan fitina. Kwanan nan a Abuja, an ba da rahoton mutuwar mutane da dama, a wani rikici da ya ɓarke tsakanin ’yan kasuwa a kasuwar Dei Dei da gungun ’yan iska da suka haɗa da ’yan acaɓa da wasu ɓarayin titi.

A ƙarshe abin ya yi muni inda aka ƙare da fashe-fashen shagunan mutane, gidaje, da ababen hawa baya ga ƙone kayayyaki na miliyoyin Nairori ƙurmus. Da ya ke ba da labarin rikicin da ya yi sanadiyar zubar da jini, wani ganau ya ce, lamarin ya faro ne bayan wani direban babur ya ɗauko wata mata inda wata babbar mota ta murƙushe matar har lahira a sakamakon gangancin ɗan acaɓar.

Matar dai tana kan babur ɗin ne a lokacin da hatsarin ya afku. An tabbatar da rasuwarta a babban asibitin Kubwa. Cikin fushi da abin da ya faru, wasu ’yan kasuwa a yankin suka banka wa babur ɗin wuta. Hakan ya kai ga harin ramuwar gayya daga wasu gungun ’yan acava da ya yi sanadiyar lalata kasuwar tare da halaka mutane da dama.

Idan za mu iya tunawa cewa, a kwanakin baya ne gwamnatin jihar Legas ta haramta wa ’yan acava zirga-zirga a ƙananan hukumomi shida. Hakan dai bai rasa nasaba da mutuwar wani matashi da ake zargin wasu ’yan acava ne suka kashe shi a unguwar Lekki da ke Jihar Legas.

An samu labarin cewa, marigayin, wanda ya kasance injiniyan sauti ne, an ƙona shi ƙurmus bayan rashin fahimta kan naira 100 da ɗaya daga cikin ’yan acaɓar.

A ra’ayinmu, dole ne gwamnati a dukkan jihohi da babban birnin tarayya su ɗauki matakan daƙile wuce gona da iri na waɗannan masu tuka babur. A cikin yin wannan kiran, duk da mun san cewa yawansu suna amfani da acaɓar ne don ciyar da iyalansu, amma dole su riƙa sa hankali wajen tafiyar da al’amuran su. Ya kamata su san cewa akwai alhaki a kansa a duk lokacin da suka yi sanadin haɗari, ko da kuwa ba a mutu ba, matuƙar dukiya ta lalata suna da alhaki. Yadda mahaya bubur ke tuƙi a tituna, kwata-kwata ba dace ba domin.

Babban hatsarin da ke tattare da ɗabi’arsu a kan babbar hanya shi ne, matsakaitan ’yan acaɓa suna da wuce gona da iri inda a wasu lokuta su kan ga cewa, sun fi ƙarfin doka kuma su kan yi alfahari da hakan. A mafi yawan lokuta jami’an tsaro na fargabar kama su. Ko da a lokacin da su ke da laifi, su kan ɓoye laifinsu su yi wa mutum taron dangi da sunan cewa ya taɓa ɗayan su.

Duk da haka, ba mu yi kira ga dakatar da ayyukan acaɓa ba musamman a yankunan karkara inda su ne kawai hanyar sufuri. A wuraren da akwai rashin isassun tsarin abeben zirga-zirgar jama’a, hana acava ba zai yiwu ba. A ra’ayinmu abin da ya kamata a yi shi ne gwamnati ta daidaita su yadda ya kamata. A halin yanzu, wasu daga cikin baburan ba su da rajista ko inshora kuma masu hawan ba su da lasisin yin aiki. Hakan ya sa suka zama barazana a kan hanyoyi. Bayan haka, gaba ɗayan haramcin zai haifar da ƙaruwar aikata laifuka da sauran munanan halaye. A namu ra’ayin, wuce gona da iri na waɗannan mahaya ya daɗe saboda babu wani abin da ake yi na saita halayensu.

Sai dai abin takaicin shi ne, Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Tarayya (FRSC) da kuma Hukumar Duba Ababen Hawa (VIO) da sauran jami’an kan hanya da alama sun yi watsi da aikin da suke yi na tabbatar da tsafta a kan titunan, kuma a yanzu sun mayar da hankali wajen samar da kuɗaɗen shiga. Akwai wani hali a nasu ɓangaren na kau da kai ga irin halin da mahaya suka shiga a kan manyan tituna. Sai dai ba a makara ba su mai da hankali kan wannan ɓangare na harkar sufuri ta hanyar dagewa da cewa sun samu horo mai kyau da lasisi tare da shigo da babura cikin rajistar da inshora idan har ana son kare sauran masu amfani da hanyar.

Haka zalika, shugabannin ƙungiyar ‘yan acava a dukkan ƙananan hukumomin da suke gudanar da ayyukansu ya kamata su wayar da kan mambobinsu kan mutunta hukuma da tuƙin tsanaki. Tunanin su na ɗaukar doka a hannu ko kaɗan yana buƙatar a daina. Al’umma ba za su iya cigaba da lamuntar rashin ɗa’a, ganganci da haɗarin da su ke haifarwa ba.

Kamar yadda muka sha ba da shawara akai-akai a wannan shafi, babu wani mutum ko ƙungiya ɗaya da ya fi karfin dokar ƙasa. Babu wanda ke da haƙƙin ɗaukar doka a hannunsa. Idan har muna son ƙasar nan ta cigaba dole sai mun haɗa hannu wajen kai ta gaba