Rikicin APC: Sanata Abdullahi Adamu ya bada haƙuri

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya bada haƙuri a kan rikicin da ya kunno kai a kwanan nan.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa kwanaki uku da su ka gabata ne dai wasu masu riqe da muƙamai a APC, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na shiyyar Arewa maso Yamma, Malam Salihu Lukman da takwaransa na Kudu maso Yamma, Isaac Kekemeke su ka zargi Adamu da ajiye su a gefe a al’amuran jam’iyyar ba tare da yi da su ba.

Sun zargi Adamu da yin abubuwa da dama waɗanda ba su dace ba a shugabancin jam’iyyar, inda su ka nuna ɓacin ransu kan yadda ya ke ɗaukar matakai shi kaɗai ba tare da aiki tare da sauran nataimakansa ba.

Sai dai kuma rahotanni sun bayyana cewa, a wata ganawa mai tsawo da ya yi da shugabanni da masu ruwa da tsaki na APC a Abuja ranar Laraba, Sanata Adamu ya fito fili ya amsa laifinsa.

Hakazalika Sanata Adamu ya bai wa duk wanda a ka vata wa haƙuri, inda ya yi alƙawarin gyara kurakurensa da kuma tafiya da kowa a wajen tafiyar da al’amuran jam’iyyar.

By Editor