Gwamna Ganduje ya yi afuwa ga fursunoni 90

Spread the love

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yi wa fursunoni casa’in afuwa.

Hakan na cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar gidajen gyaran hali ta Nijeriya shiyyar Kano Musbahu Lawan Kofar Nassarawa ya fitar.

Sanarwar ta ce, gwamnan ya yi musu afuwar ne a ziyarar bikin Babbar Sallah da ya kai gidan gyaran halin.

Kazalika sanarwar ta ce, cikin mutanen da gwamnan ya yi wa afuwa har da mutane goma sha uku da aka yanke wa hukuncin Ƙisa.

Musbahu Lawan ya kuma ce gwamna Ganduje ya biya wa mutane saba’i’n da bakwai diyyar kuɗin da ake binsu domin fita daga gidan gyaran halin baya ga mutane 13 da a baya aka yanke wa hukuncin kisa, amma ganin halayensu sun gyaru ya sanya gwamnan ya yi musu afuwa.

Sai kuma wasu ɗaurarru uku waɗanda aka yanke wa hukuncin kisa amma gwamnan ya yi musu afuwa zuwa ɗaurin rai da rai.

By Editor