Daga ABBA YAKUBU ABUBAKAR a Bauchi
A wani ɓangare na bukin cika shekaru biyu da kafuwar ƙungiyar haɗin kan matasan Arewa masu aiki da zaurukan sada zumunta na soshiyal midiya ta Arewa Media Writers ta shirya gudanar da wata gagarumar bita ta wuni biyu a Jihar Bauchi, domin ƙara wayar da kan ýan ƙungiyar dabarun amfani da zaurukan sada zumunta da yadda za su ci moriyar damar da ake samu.
Taron wanda aka fara shi da yammacin ranar Jumma’a a babban ɗakin taro na otel din Zaranda ya samu halartar ýaýan ƙungiyar daga dukkan jihohin Arewa, waɗanda suka fara shiga Bauchi tun a jiya Alhamis.
Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Kwamred Abba Sani Pantami ya bayyana cewa, wannan bita wani ɓangare ne na cimma manufofin ƙungiyar da suka haɗa da samar da horo kan aikin samar da bayanai da yaƙi da yaɗa labaran ƙarya a kafofin sadarwar zamani, da kuma haɗa kan matasan wajen yin magana da murya ɗaya kan duk wani al’amari da ya shafi yankin Arewa da al’ummar ta da ke zaune a sauran sassan ƙasar nan.
Ƙungiyar ta gayyato mashahuran malamai, fitattun ýan jarida da masu faɗa a ji a harkokin watsa labarai, kuma ana sa ran faɗakar da matasa kan hanyoyin yaƙi da labaran ƙarya a kafofin sada zumunta. Yadda ake rubutu da aikin jarida, na yaɗa labarai a kafofin sada zumunta. Tasirin kafofin sada zumunta a siyasar Najeriya, tsaron kasa, da amfanin ta ga al-umma.
Sauran darussan da za a duba sun haɗa da yadda ake neman kuɗi, da aiki a kafofin sada zumunta. Tasirin haɗin kan marubutan Arewa, da kuma muhimmancin harshen uwa, ga tasirin hulda da jama’a a yanar gizo.
Ana sa ran Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Abdulkadir Bala Mohammed da tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Sr Abdu’Aziz Yari Abubakar, Shettiman Zamfara a matsayin ɗaya daga cikin manyan baƙi a wannan taron.
