Daga ABUBAKAR M TAHEER a Jigawa
Jami’an ‘Yan Sandan Jihar Jigawa sun sanar da damƙe ƙasurgumin mai safarar miyagun ƙwayoyi a ƙaramar Hukumar Auyo.
A cikin wata sanarwar manema labarai da Jami’an hulɗa da jama’a na hukumar, SDP Shiisu Adam ya sa wa hannu ya bayyana cewa, sun yi nasarar damƙe matashin ne a Garin su na Auyo.
Matashin mai Suna Auwal Muhammad Sani mai shekaru 22, ya bayyana cewa yana samun waɗannan muggan ƙwayoyi ne daga wani mai safarar ƙwayoyin mai suna Sule Kulle da ke ƙauyen Adaha.
An samu a tattare da shi ƙullin wiwi guda 265, sai ƙwayar D5 guda 89, ƙwayar BZ guda 60 da kuma rezlar 12.
Ya zuwa haɗa wannan labari, ‘yan sanda sun tabbatar da cigaba da bincike a kansa inda a ƙarshe za su gurfanar da shi gaban kuliya.
