Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse
Gwamnatin Jigawa ta ce gidaje 1,300 ne guguwar ta lalata a Ƙaramar Hukumar Kafin Hausa.
Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya bayar da rahoton cewa, lamarin da ya faru a ranar Talata da daddare, ya yi varna sosai.
Mataimaki na musamman ga Gwamna Muhammad Badaru kan ci gaban al’umma da taimakon jama’a, Hamza Muhammad, ya shaida wa NAN a ranar Asabar cewa, sama da gidaje 1,300 ne ibtila’in guguwar ya afkawa, inda wasu suka rushe gaba ɗaya, wasu kuma suka lalace.
Muhammad ya ce guguwar ta kuma lalata wasu sassan babban asibitin yankin da matatar ruwa da kuma makarantu.
“Daga rahoton tantancewar da na samu, baya ga waɗannan, guguwar ta kuma lalata rufin babban asibitin Kafin Hausa na ɗakunan haihuwa da na gaggawa da na wasu makarantun yankin.
“Haka kuma ya sauke wasu tankunan ruwa na sama, da kuma ɗaya daga cikin antenar sadarwa a yankin,” inji Muhammad.
Sai dai ya ƙara da cewa an kai marasa lafiya a ɗakin haihuwar lafiya zuwa wasu wuraren kiwon lafiya.
Mataimakin ya kuma bayyana cewa, gwamnatin jihar tare da haɗin gwiwar Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar, SEMA da kuma Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA, sun kasance a yankin tun a ranar Laraba, inda suka tantance irin varnar da bala’in ya yi.
Wannan a cewarsa, domin bai wa gwamnati da hukumomi damar sanin irin ɓarnar da guguwar ta haddasa, da nufin shiga tsakani da kuma bayar da tallafi ga waɗanda abin ya shafa.
