Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Zave Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, a ranar Talata, ta yi alƙawarin gudanar da zaɓuka mafi kyawu a Nijeriya a shekarar 2023.
Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bada wannan tabbacin a lokacin da ya karvi baƙuncin tawagogin ‘ International Republican Institute, IRI, da na National Democratic Institute, NDI, a Abuja.
Ya ce taron shi ne na farko da INEC ta shirya bayan zaɓen gwamnan jihar Osun da aka yi ranar Asabar, ya kuma bada tabbacin cewa za ta inganta nasarorin da ta samu a zaɓukan da ke tafe.
“Mun samu ƙwarin gwiwa da kalamanku masu kyau, amma har yanzu akwai sauran aiki a gaba.
“Muna tabbatar muku da cewa za mu ƙara zage damtse wajen yin aiki tuƙuru don ganin mun gudanar da babban zaɓen 2023 cikin nasara.
“Na saurari wasu batutuwan da aka gabatar amma watakila, idan muka shiga zaman aiki za a samu damar mayar da martani ga wasu batutuwa,” inji shi.
“Mun yi alƙawarin cewa zaɓen Osun zai yi kyau, kuma ga shi zaven Osun ya yi kyau. Mun yi alƙawarin cewa babban zaɓe na 2023 zai kasance mafi kyawun zaven da muka taɓa yi kuma mun himmatu wajen ganin mun samar da mafi kyawun zaɓe a koyaushe,” inji shi.
