Matashi ya yi wa ƙanwarsa fyaɗe a Gombe

Spread the love

’Yan sanda a Jihar Gombe sun kama wani matashi mai suna Abubakar Hamidu, ɗan shekaru 35 da ke zaune a Unguwar Jauro Abare, da zargin yi wa ƙanwarsa fyaɗe har sau biyu a lokuta daban-daban.

Rahotanni sun rawaito cewa, da ya ke gabatar da wanda ake zargin ga manema labarai, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Gombe, Ishola Babatunde Baba’ita, ya ce, wani mai suna Muhammad Hamza ne ya shigar da ƙarar matashin a ranar 19 ga watan Yulin da mu ke ciki.

Baba’ita ya ce, mai shigar da ƙarar wanda ke zaune a Unguwar Kasuwar Mata, ya kai wa ’yan sanda ƙorafin cewa wanda ake zargin ya yi lalata da ƙanwar tasa ce karon farko a wani gida da ya zama kufai a Unguwar ta Jauro Abare.

Kwamishinan ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan, ASP Mahid Mu’azu, ya ce, an sake kama matashin karo na biyu yana aikata laifin da ƙanwar tasa a bakin wani tafki.

A cewarsa, da zarar sun kammala bincike za su tura wanda ake zargin zuwa kotu domin ya fuskanci hukunci.

By Editor