Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato
Ɗan takarar Shugabancin Nijeriya na Jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya aike da saƙon taya murna ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar bisa zagayowar ranar haihuwarsa.
Mai Alfarma Sarkin na Musulmi wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Ƙoli ta Addinin Musulunci a Nijeriya, ya cika shekaru 66 a duniya ranar 24 ga watan Agustan 2022.
A saƙon taya Sarkin Musulmin murnar ranar haihuwarsa a shafin sa na Tiwita, Wazirin Adamawa ya ce a madadinsa da iyali, yana taya murna gare shi sannan yana addu’ar Allah Ya ƙara masa lafiya domin ci gaba da jagorancin al’ummar Musulmin ƙasar nan.
Atiku ya kuma jinjina wa Muhammadu Sa’ad Abubakar bisa ƙoƙarinsa na tabbatar da tattaunawar fahimtar juna tsakanin addinai.
